Hotunan ango da amarya da basu kashe N50k a bikinsu ba, sun saka tsofaffin kaya

Hotunan ango da amarya da basu kashe N50k a bikinsu ba, sun saka tsofaffin kaya

  • Wani dan Najeriya mai suna Gborienemi Mark-Charles II, ya ce ya kashe kasa kudin da bai kai dubu hamsin ba wurin yin aurensa
  • Gborienemi ya kara da cewa matarsa ta ja masa kunne kan kada ya barnatar da kudin wurin kayatar da baki da abinci
  • Ta shawarcesa da ya narka kudin a kan kasuwancinsa kuma sun saka tsofaffin kaya wurin auren tare da karanta yawan baki
"Mata ta ce ta shawarce ni da kada in barnata kudina akan shagalin, amma in kara akan kasuwanci na" wani mutum dan Najeriya ya bayyana yadda ya kashe kasa da N50,000 a shagalin bikin sa.

Wani mutum mai suna Gborienemi Mark- Charles, daga jihar Bayelsa, ya bayyana yadda ya kashe kasa da N50,000 a shagalin auren shi.

Hotunan ango da amarya da basu kashe N50k a bikinsu ba, sun saka tsofaffin kaya
Hotunan ango da amarya da basu kashe N50k a bikinsu ba, sun saka tsofaffin kaya. Hoto daga Gborienemi Mark Charles II
Asali: Facebook

Kamar yadda Gborienemi ya bada labari, matarsa ce ta shawarce shi da kada ya barnata dukiyar shi a shagalin auren su, da haka gara ya narka a kasuwancin shi.

Kara karanta wannan

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

"Masoyina, ina rokon alfarma, a shagalin auren mu, ba na so ka barnata kudin ka wajen siyan rigunan amarya, abinci, abun sha, hayar wurin shagali, kwalliya da sauran abubuwan da basu taka kara sun karya ba. Da haka, gara ka kara kudin a kasuwancin ka"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Baya ga kudin sadaki da na biya, mata ta bata gayyaci bakin da suka kai goma ba, daga dangin uwa da uba. Mun saka tsofaffin kayan da muke da su a gida.
"An daura mana aure, sannan muka sa hannu a takardar shaidar auren mu.
"Ubangiji kadai zai maka haka. Mata irin wannan suna wahalar samu wa a zamanin nan.Amma ina tunanin ni mutum ne mai sa'a.
"Da izinin Ubangiji, na narka kudin da ya kamata in yi shagalin biki da su a kasuwanci na. Kuma gashi kasuwancin nawa yana cigaba da habaka. Sannan muna rayuwar aure cikin farinciki," ya bayar da labari.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

A wani labari na daban, ana tuhumar wani dalibi dan kasar Kenya mai shekaru 21 da zargi kan cin zarafin mijin wata wacce ake zargi da zama masoyiyar sa, bayan ya tura mishi hoton tsiraici na sirrin matar sa.

Wanda ake zargin, Steven Wanjohi Kamande, ya bayyana gaban babban alkalin majistare Wendy Kagendo na kotun shari'a ta Milimani a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ya musanta laifuka ukun da ake zargin sa da su, na tura mishi bayanin kanzon kurege, barazana ga rayuwar shi da gangancin yada ababen da basu dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel