Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da Sheikh Ahmad Gumi

Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da Sheikh Ahmad Gumi

A ranar Asabar, gobara ta kama gidan fitaccen malamin addinin Musulunci nan mazaunin garin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi.

An tattaro yadda gobarar ta taba kwanon rufin wani bene.

Tuni malamin ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, "yin Allah ne" kuma ba a san me ya haddasa gobarar ba, saboda babu wutar lantarki lokacin da al'amarin ya auku."
Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Sheikh Ahmad Gumi
Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Sheikh Ahmad Gumi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ga wasu muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da malamin:

Tsatson shi

Sheikh Ahmad Gumi shi ne babban dan sanannen malamin addinin Musulunci, kuma tsohon babban alkalin Musulunci na yankin arewacin Najeriya, Abubakar Mahmud Gumi.

An haife shi a watan Oktoba 1960, sannan yana bada fatawa da fassarar Alkur'ani a masallacin Sultan Bello cikin garin Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Aikin soja

Ahmad Gumi ya yi ilimin sakandirin shi a makarantar Sardauna Memorial College (SMC), daga baya ya tafi jami'ar Ahmadu Bello, inda ya karanta likitanci.

Bayan kammalawa, malamin ya wuce Saudi Arabia don cigaba da karatun addinin shi a jami'ar Umm al-Qura, inda ya karanta fassara da tafsirin Alkur'ani mai girma.

Sheikh Gumi ya shiga makarantar horar da hafsoshin soja, inda yayi aiki a sashin lafiya na sojojin Najeriya (NAMC) a matsayin likita, sannan yayi ritaya a kyaftin.

Sulhu da 'yan bindiga

Tsohon kyaftin na sojojin ya dade ya na shiga labarai, saboda burin sa na ganin an zauna lafiya da tarin 'yan ta'adda a maboyar su a Kaduna, Katsina da jihar Zamfara.

Wanda yayi kokarin ganin an saki wadanda aka kama, musamman dalibai 27 da aka yi garkuwa da su daga makatantar koyar da gandun dabbobi ta Najeriya a jihar Kaduna cikin watan Maris na shekarar da ta gabata.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Malamin ya sha caccaka daga tarin 'yan Najeriya, wadanda suka hada da mulkin Buhari saboda irin matsayin shi ga 'yan bindiga.

Halin sukar Buhari

Sheikh Gumi ya kasance mai matukar sukar gwamnatin kan rashin iya mulki

A shekarar 2019, malamin yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya sauka saboda yadda gwamnatin sa ta gaza.

Ya musanta jita-jita kan cewa yana sukar jam'iyyar APC ne saboda tausayin jam'iyyar adawa ta PDP.

Lokacin da gwamnatin tarayya ta haramta Twitter a shekarar da ta gabata, Gumi ya bukaci gwamnatin tarayyan ta zama mai nuna halin girma wurin amince wa da caccaka.

Ya ce:

"Ya kamata gwamnatin tarayya ta nuna halin girma game da matakan da take dauka, ba za su iya yaki da kafar sada zumunci ba. Ya kamata gwamnatin tarayya ta zamo ginshiki mai amsar kushe."

Asali: Legit.ng

Online view pixel