Zaben Abuja: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a rumfunan zaben fadar Shugaban kasa

Zaben Abuja: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a rumfunan zaben fadar Shugaban kasa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kuri'un rumfunan zabe biyu dake fadar shugaban kasa a zaben ciyamomi da kansilolin dake gudana da birnin tarayya, Abuja.

APC ta lallasa jam'iyyar hamayya PDP a runfunan zabe na 021 da 022 dake karamar hukumar Abuja Municipal, rahoton PremiumTimes.

Fadar shugaban kasa na dauke da gidaje da ofishoshin manyan jami'an gwamnati da kuma shugaban kasa da mataimakinsa.

Zaben Abuja: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a rumfunan zaben fadar Shugaban kasa
Zaben Abuja: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a rumfunan zaben fadar Shugaban kasa
Asali: Original

Jami'an hukumar INEC dake rumfar PU 021 sun sanar da cewa APC ta samu kuri'u 79 a akwatin Ciyaman yayinda PDP ta samu 36.

A nan Kansila kuwa, APC ta samu kuri'u 84 yayinda PDP ta samu kuri'u 30.

Kara karanta wannan

Zaben Abuja: Wani dan jam'iyya ta buge wata mata da ta zo zabe da babur

A PU 022, APC ta samu kuri'u 41 yayinda PDP ta samu 33 a akwatin ciyaman. Hakazalika APC ta samu kuri'u 44 inda ta doke PDP mai kuri'u 30 a akwatin Kansilan yankin.

A PU 121, mutum daya kacal ya kada kuri'arsa kuma PDP ya dannawa.

Amma a rumfa ta hudu, PU 122, babu wanda ya fito zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel