Zaben Abuja: Wani dan jam'iyya ta buge wata mata da ta zo zabe da babur

Zaben Abuja: Wani dan jam'iyya ta buge wata mata da ta zo zabe da babur

  • Ana fargabar wata mata ta mutu a Abuja yayinda taje kada kuri'arta a unguwar Karu, daga karamar hukumar AMAC
  • Wani dan siyasa mai wasa da babur ya doke ta a harabar rumfar zaben

Abuja - Wani matashin daya daga cikin manyan jam'iyyun siyasan Najeriya a birnin tarayya Abuja ya buge wata mata da tazo zabe da babur dinsa.

Vanguard ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne a rumfar zaben PU048, Salasi gaban Post Office, a Karu, AMAC.

Matashin rike da tutar jam'iyarsa yana wasa da babur ne lokacin da ya make matar.

An tattaro cewa kai tsaye sauran jama'a suka damke matashin kuma suka mikashi ga jami'an tsaro.

Zaben Abuja: Wani dan jam'iyya ta buge wata mata da ta zo zabe da babur
Zaben Abuja: Wani dan jam'iyya ta buge wata mata da ta zo zabe da babur
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Jirgin Ƙasa Ya Yi Tsayawar Dole a Daji Saboda Ɓarnar Da Ƴan Daba Suka Yi a Hanya

Yan takarar kujeran Ciyaman 55, Kansila 363 da suke karawa yau

Akalla masu neman kujeran shugabannin kananan hukumomi 55 da masu neman kujerar Kansila 363 yayinda mutum milyan 1.4 zasu musharaka a zaben birnin tarayya Abuja yau Asabar.

Hukumar zaben Najeriya INEC ce zata gudanar da zaben kananan hukumomi shida da kujerun kansiloli 62.

Diraktar cibiyar bibiyar zaben CTA, . Faith Nwadishi, a hira da manema labarai ranar Juma'a a Abuja ta bayyana cewa INEC ta ce jam'iyyun siyasa 14 zasu yi musharaka a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel