Fusatattun jama'a sun kai wa tawagar dan majalisar su na tarayya farmaki a Jigawa

Fusatattun jama'a sun kai wa tawagar dan majalisar su na tarayya farmaki a Jigawa

  • Fusatattun jama'a mazauna yankin Birnin Kudu a jihar Jigawa sun kai wa tawagar dan majalisar su farmaki
  • A cewar jama'ar, dan majalisa Magaji Da'u ya gaza yi musu wakilci nagari kuma ya zo ne yanzu yayin da zabe ke gabatowa
  • Jama'ar sun dinga caccaka da sukar dan majalisar tare da rufe hanyar da zai wuce, lamarin da ya janyo arangama tsakanin magoya bayansa da jama'ar

Jigawa - Jama'ar da suka kada wa dan majalisar wakilai, Magaji Da'u kuri'a sun kai wa tawagarsa farmaki a ranar Alhamis a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa kan zarginsa da rashin wakilci nagari.

'Yan sanda sun ce, Da'u, wanda ke wakiltar mazabar Birnin Kudu da Buji a tarayya, ya na kan hanyarsa ne ta zuwa wani taron siyasa a yankin yayin da aka kai wa tawagarsa farmaki.

Kara karanta wannan

Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko

Fusatattun jama'a sun kai wa tawagar dan majalisar su na tarayya farmaki a Jigawa
Fusatattun jama'a sun kai wa tawagar dan majalisar su na tarayya farmaki a Jigawa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya sanar da Premium Times cewa, akasin rahotanni da ke yawo kan cewa 'yan bindiga ne suka kai wa tawagar hari, "tushen faruwar al'amarin shi ne rashin jituwa tsakanin kungiyoyin siyasa."

“An dakile aukuwar lamarin kuma 'yan sanda sun cafake wasu daga cikin wadanda ake zargi ta hada hargitsin," kakakin rundunar 'yan sandan yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun rufe hanyar da dan majalisar zai bi ya tafi yankin Kukuma domin halartar wani taron siyasa.

Jama'ar sun dinga zage-zage tare da maganganu marasa dadi, inda suke zargin dan majalisar da rashin wakilci nagari kuma da yin watsi da wadanda ya ke wakilta har sai yanzu da ya bayyana saboda zaben 2023 ya na gabatowa.

Wannan al'amarin ya haifar da arangama tsakanin jama'ar da magoya bayan dan majalisar da ke tawagarsa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tafiya a mota: Gwamna ya makale a hanyar Kaduna, jirgi ya dauke shi cikin gaggawa

Har zuwa yammacin ranar Alhamis, ba a samu dan majalisar ba ta wayar salula yayin da aka kira shi.

Tirkashi: Yadda fusatattun matasa a jihar Kebbi suka dinga sanyawa hotunan shugaba Buhari wuta

A wani labari na daban, wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya nuna yadda wasu fusatattun matasa a jihar Kebbi suke kone hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma na gwamnan jihar Atiku Bagudu.

Bayan kone hotunan shugabannin biyu, matasan sun kuma koma kan kayayyakin gwamnati, yayin da suke yin ihun cewa babu wuta, babu aikin yi.

Matasan wanda suke ta faman yawo a cikin Birnin Kebbi babban birnin jihar ta Kebbi, sun zagaye duka garin suna wannan zanga-zanga tare da Allah wadai da gwamnatin da suke ciki ta gwamna Atiku Bagudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel