Tirkashi: Yadda fusatattun matasa a jihar Kebbi suka dinga sanyawa hotunan shugaba Buhari wuta

Tirkashi: Yadda fusatattun matasa a jihar Kebbi suka dinga sanyawa hotunan shugaba Buhari wuta

- Wasu fusatattun matasa a jihar Kebbi sun hada wata zanga-zanga inda suka dinga bi layi-layi suna kone hotunan shugaba Buhari dana gwamnan jihar Atiku Bagudu

- Matasan sun dauki wannan mataki ne bayan matsalar rashin wuta da rashin aikin yi da suke fama da shi a fadin jihar

- Wani bidiyo da ya dinga yawo na matasan a lokacin da suke zanga-zangar ya nuna yadda matasan suke ihun babu aiki babu wutar lantarki

Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya nuna yadda wasu fusatattun matasa a jihar Kebbi suke kone hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma na gwamnan jihar Atiku Bagudu.

Bayan kone hotunan shugabannin biyu, matasan sun kuma koma kan kayayyakin gwamnati, yayin da suke yin ihun cewa babu wuta, babu aikin yi.

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda wani masifaffen Zakara ya kashe uwargijiyar sa har lahira

Matasan wanda suke ta faman yawo a cikin Birnin Kebbi babban birnin jihar ta Kebbi, sun zagaye duka garin suna wannan zanga-zanga tare da Allah wadai da gwamnatin da suke ciki ta gwamna Atiku Bagudu.

A Najeriya dai ana ta fama da matsaloli irinsu rashin tsaro, matsalar rashin aikin yi, wutar lantarki da dai sauransu, wannan dalilin ne yasa wasu matasan suke daukar doka a hannunsu wajen yin zanga-zanga koda gwamnati za ta gani ta canja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel