BUK: Ɗalibin ajin ƙarshe ya yanke jiki ya faɗi ya mutu lokacin da ya ke shirin zuwa masallaci a ranar Juma'a

BUK: Ɗalibin ajin ƙarshe ya yanke jiki ya faɗi ya mutu lokacin da ya ke shirin zuwa masallaci a ranar Juma'a

  • Wani dalibi da ke ajin karshe a Jami’ar Bayero da ke Kano, dan asalin Jihar Bauchi, Babangida Ahmad ya fadi ya mutu a ranar Juma’a, 28 ga watan Janairu
  • Ahmad yana shirin tafiya masallaci don yin sallar asubahi a cikin dakin dalibai na jami’ar lamarin ya auku da shi kamar yadda sakataren watsa labaran jami’ar, Bala Abdullahi ya shaida
  • Sakataren ya bayyana ta wata takarda da ya saki a ranar Juma’ar, inda yace hukumar jami’ar ta tuntubi iyayen sa kuma an zarce da shi garin su don birne shi

Jihar Kano - Wani dalibi da ke ajin karshe a fannin Library and Information Science a Jami’ar Bayero da ke Kano ya rasu, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Dalibin mai suna Babangida Ahmad dan asalin Jihar Bauchi ya fadi ya rasu ne a cikin dakin dalibai da ke Jami’ar da safiyar Juma’a, 28 ga watan Janairu yayin da yake shirin tafiya sallar asubahi.

Sakataren watsa labaran jami’ar, Bala Abdullahi ne ya shaida hakan ta wata takarda da ya saki a ranar Juma’a, 28 ga watan Janairu.

'Dalibin ajin ƙarshe a BUK ya yanke jiki ya faɗi ya mutu cikin ɗakin ɗalibai
'Dalibin ajin ƙarshe a BUK ya faɗi ya mutu cikin ɗakin ɗalibai a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kamar yadda LIB ta ruwaito takardar ta zo:

“Hukumar makarantar ta tuntubi iyayen sa dangane da faruwar lamarin kuma an wuce da shi garin su don birne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.”

Tun safe ya fadi aka zarce da shi asibitin makarantar

Bayan tuntubar abokin sa, ya ce Marigayi Babangida ya bar dakin su ne da misalin karfe 4:30am inda ya fadi daga nan aka zarce da shi asibitin makarantar don kulawa da shi. Ya ce ashe gawar sa aka wuce da ita asibitin.

Kara karanta wannan

Ya yi karatu a makarantarmu – Jami’ar Amurka ta raba gardama kan Digirin Bola Tinubu

Ya kara da cewa:

“Tun kafin mutuwar sa, ya dade yana zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) don ganin likita amma ba a san ciwon da ke damun sa ba.
“Kamar yadda takardar asibiti ta nuna, ya je asibitin AKTH wurin sau bakwai a shekarar da ta gabata, kuma ranar 10 ga watan Janairun 2022 ce ranar karshe da ya je ganin likitan. Ya kamata ya koma AKTH a ranar 7 ga watan Fabrairun 2022.
“Sai dai hukumar makarantar ta wuce da gawar mamacin garin su, Misau da ke Jihar Bauchi don a birne shi.”

Shugaban jami’ar ya mika sakon ta’aziyyar sa

Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yi wa iyaye da abokan dalibin ta’aziyya a maimakon daukacin jami’ar kuma ya yi masa fatan dacewa da Aljannar Firdaus.

Kowa ya san marigayi Babangida a matsayin mutum mai kirki, fara’a da son jama’a kuma yana da kyakkyawar alaka da abokan karatun sa.

Kara karanta wannan

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

'Dalibin ajin ƙarshe a BUK ya yanke jiki ya faɗi ya mutu cikin ɗakin ɗalibai
Dallibin BUK na ajin karshe ya fadi ya mutu. Hoto: LIB
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel