Neja: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun ƙwato shanu 300

Neja: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun ƙwato shanu 300

  • Jami’an tsaro a Jihar Neja sun halaka ‘yan bindiga da dama da suka addabi wasu garuruwa da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro
  • Ayyukan jami’an tsaron sun kawo nasarar kwato dabbobi 500 a garuruwa kamar Kuchi, Galadiman Kogo, Allawa da Erena inda da taimakon mafarauta aka wuce da dabbobin Minna
  • Shanu 5 sun mutu kafin su isa Minna saboda nisa da kuma tsukewar motar da aka zubo su kamar yadda Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar, Emmanuel Umar ya shaida

Neja - Jami’an tsaro na Jihar Neja sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama da suka dade suna addabar wasu garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Ayyukan jami’an tsaron sun janyo an samu nasarar kwace dabbobi 500 a garin Kuchi, Galadiman-Kogo, Allawa da garin Erena da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro.

Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga a Neja, sun kwato shanu 300
Neja: Jami’an tsaro sun halaka ‘yan bindiga, sun kwace shanu 300. Hoto: Daily Trust
Asali: Getty Images

An kwashe dabbobin sannan aka garzaya da su Minna, babban birnin jihar da taimakon mafarauta.

Shanu biyar sun mutu kafin a isa dasu Minna saboda matsewar abin hawan da aka zuba su ciki da kuma nisa.

An samu shanu 300 da tumaki fiye da 100

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da harkokin cikin gida na jihar, Emmanuel Umar ya shaida yadda aka samu nasarar kwaso dabbobin wadanda ciki akwai shanu 300 da tumaki fiye da 100.

A cewarsa za a ajiye dabbobin karkashin kulawar Ma’aikatar Dabbobi ta Jihar.

A cewarsa, yayin da aka halaka ‘yan bindiga da dama, wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu amma bai sanar da yawansu ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

Ya ce yanzu haka ana ta kokarin ganin yadda za a tallafa wa iyalan jami’an tsaron da aka halaka.

Kwamishinan ya kula da yadda gwamnatin jihar ta gama shirya hanyoyin da zata gano asalin masu dabbobin don a basu ko kuma su shiga cikin dukiyar jihar.

An samar wa rundunar ‘yan sandan sabbin kayan yaki da motoci don su tallafa wurin yakar ta’addanci a jihar

Umar ya kula da yadda rashin tsaro a jihar zai gyaru matsawar aka kawo karshen ‘yan bindiga, masu satar dabbobi, masu garkuwa da mutane da sauransu.

Sai dai Daily Trust ta tattaro bayanai akan yadda rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta gama samun kayan yaki daga hedkwatar ‘yan sandan don kawo karshen ‘yan ta’addan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da cewa an samar da kayan yaki har da ababen hawa biyar tare da motocin yani daga hedkwatar ‘yan sanda.

A cewarsa ana fatan sabbin kayan yakin za su taimaka wa rundunar wurin kawo karshen ta’addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel