Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku
- Yayin da ake shirye-shiryen zaben 2023 mai zuwa, jam'iyyun siyasa na ci gaba da fuskantar tasgaro
- Jam'iyyar PDP, ta shiga wani lamari mai kama da matsi yayin da 'yan takara daga yankuna ke nuna sha'awarsu
- Gwamnonin kudu sun ce sam babu ruwansa da dan takara daga Arewa, dole ne PDP ta tsayar da dan takara daga kudu
FCT, Abuja - Ba kamar 2019 inda jam’iyyar PDP ta ba da tikitin takarar shugabannci kasa ga 'yan Arewa ba, har yanzu ba a cimma kwakwaran matsaya ba game da wani shiyya ne zai fitar da dan takara a zaben shugaban kasa na 2023 da ke karatowa.
Wannan matsalar ta samo asali ne inda wasu masu fada a ji a jam’iyyar suka dage kan cewar sune ya kamata su fito takarar shugaban kasa daga yankin kudu.
Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da takwaransa na jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, na daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP da suke son kawo cikas.
Matsayar PDP a baya
Idan ba a manta ba, Kwamitin Zartaswa na kasa na PDP a taronsa na 89 da ya gabata a watan Fabrairun 2020, ya kafa kwamitin mutum 14 da zai duba dalilan da ya sa jam’iyyar PDP ta sha kaye a zaben 2019, domin daukan mataki a zaben gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ko da yake kwamitin na Bala Mohammed ya shawarci shugabannin jam’iyyar da su bada tikitin takarar shugaban kasa ga dukkan shiyyoyi guda shida na kasar, amma gwamnonin PDP daga kudu suna kokarin ganin cewa shiyyarsu ce ta kawo shugaba a 2023.
Manufar PDP na gwangwajewa wajen zaban nagartaccen dan takara shi ne domin a sama wanda zai iya tunkarar dan takarar jam'iyya mai ci ta APC a zaben na 2023.
Vanguard ta tattaro cewa gwamna Wike ya na ta zaman tattaunawa da sauran gwamnonin PDP na Arewa kan bukatar su goya ma kudu baya kamar yadda aka yi a taron shugaban kasa da ya gudana a Fatakwal a shekarar 2018.
A taron ne aka ayyana Atiku a matsayin dan takarar da jam'iyya ta tsayar, gwamnan jihar Ribas ya fito fili ya nuna shi yana goyon bayan takwaransa na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, wanda shine ya zo na biyu bayan Atiku a wancan lokacin.
Tun daga lokacin da Atiku ya samu nasarar zama tsayeyen dan takara, gwamna Wike bai yi wata-wata ba wajen nuna goyon bayansa sannan ya yi kira ga sauran mambobin jam'iyyar da su hada kai domin ciyar da jam'iyyar gaba.
Gwamnan kudu ya yi watsi da Atiku
Wani babban mai taimaka wa gwamnan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida a wata tattaunawa da akayi da shi ta wayar tarho jiya ya bayyana cewa:
“Gwamna Wike yana kokarin fadakarwa akan a yi adalci.
‘’Bayan haka, ya na da kwakwaran hujjoji ganin cewa kujera ta koma kudu a 2023, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai kare wa’adinsa na biyu, kuma bai kamata ace dan Arewa ne za a tsayar a matsayin magaji ba ko da kuwa yafito daga jam'iyyar PDP ne.
"Shi yasa Gwamnan yake son jam’iyyar ta yi dubi ga 'yan Kudu domin muna da shugabanni da suka cancanci wannan kujera wadanda za su iya dawo da tattalin arzikin kasar nan."
A kwanakin baya ne dai aka ce Atiku ya gana da Wike a kan batun takararsa ta shugaban kasa kawai sai gwamnan na jihar Ribas ya ce wa Wazirin Adamawa ya jira har sai shugabannin jam’iyyar sun dauki matsaya a kan shiyya tukuna.
Gwamna Wike, ya kuma bukaci Atiku da ya shirya tsaf domin marawa dan takarar Kudu baya idan har jam’iyyar ta yanke shawarar mika kujera Kudu a 2023. Babu tabbas ko Atiku ya amince da ba dan kudu goyon bayan a zaben na 2023.
Kungiyar Inyamurai ta yi watsi da Atiku
A wani labarin, Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta yi watsi da kudurin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na yin wa'adi daya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
A cewar kungiyar, wannan shawara wata dabara ce da za ta hana yankin Kudu maso Gabas cimma manufofin siyasarta na farko na neman kujerar shugaban kasa.
Ku tuna cewa Raymond Dokpesi, na hannun daman mai neman takarar shugaban kasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai mulki Najeriya ne na tsawon shekaru hudu kawai idan har aka zabe shi a 2023, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng