'Yan bindiga sun tare hanya sun sace mutane 5 a Jihar Yobe

'Yan bindiga sun tare hanya sun sace mutane 5 a Jihar Yobe

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a kauyen Madiya da ke karamar hukumar Gujiba a cikin Jihar Yobe
  • An samu labarin yadda ‘yan bindigan suka sanya bulo a wuraren Madiya kafin su yi garkuwa da mutanen
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarin ya tabbatar da aukuwar lamarin ranar a Laraba

Jihar Yobe - ‘Yan bidiga sun yi garkuwa da mutane 5 a kauyen Madiya da ke karkashin karamar hukumar Madiya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An samu rahotanni akan yadda ‘yan bindigan suka sanya bulo a yankin Madiya da ke jihar kafin su yi garkuwa da jama’an.

'Yan bindiga sun tare hanya sun sace mutane 5 a Jihar Yobe
'Yan bindiga sun sace mutum 5 a Jihar Yobe. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka kashe da dama

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya saki ranar Laraba.

Kakakin ya lissafo wadanda aka yi garkuwa da su

The Cable ta ruwaito yadda Abdulkarim ya lissafo sunayen wadanda aka sace inda yace akwai mataimakin shugaban makarantar firamaren Buni Yadi, Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da Hajiya Gana.

A cewar kakakin, lamarin ya auku ne da misalin karfe 8:20 na safiyar ranar Talata inda wani Mala Boyema ya kai wa ofishin ‘yan sandan yankin rahoto.

A cewar Kakakin, Boyema ya samu nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigan bayan ya labe a wasu bulollukan su da suka sa a Madiya.

Sun saki daya daga cikin wadanda suka sata

Ya kara da shaida yadda ‘yan bindigan suka saki Kachalla daga bisani.

Jihohi da dama da ke kasar nan suna ci gaba da fama da matsalolin garkuwa da mutane da amsar makudan kudade a matsayin kudin fansa musamman a yankin arewa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

An kashe sifetan ‘yan sanda yayin musayar wuta da ‘yan bindiga

A wani labarin, Sifetan ‘yan sanda, Omolayo Olajide da wasu ‘yan bindiga biyu sun rasu a ranar Talata yayin musayar wutar da ta auku tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda harbe-haren ya auku tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindigan a dajin Saala Orile da ke karamar hukumar Yewa ta arewa da ke Jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ya ce bayan sun samu kiran gaggawa a ofishin ‘yan sanda na Ayetoro, Bernard Ediogboyan, ya jagoranci yaran sa da rundunar JSIS zuwa inda ‘yan bindiga suke ta’addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel