Karshen 2021: Bankunan Najeriya mafi daraja da wadanda suka tafka asara a 2021

Karshen 2021: Bankunan Najeriya mafi daraja da wadanda suka tafka asara a 2021

  • An bayyana jerin manyan bankunan Najeriya mafi daraja a shekarar 2021 tare da bankunan Guaranty Trust da Zenith a kan gaba a jerin sunayen
  • An kididdige darajar bankunan ne ta hanyar amfani da nawa aka kara a kan jimillar farashin hannun jari zuwa ranar Juma’a 31 ga Disamba, 2021
  • Hannun jarin bankunan Najeriya ya kasance daya daga cikin mafi yawan ciniki a musaya a Najeriya da kuma tantance yadda kasuwa ta kasance

An ba da rahoton cewa bankin Zenith shi ne bankin kasuwanci mafi daraja da aka jera a kan teburin musaya ta Najeriya (NGX) na 2021 da kuma rukunin bankunan Guaranty Trust da First Bank.

Ya jagoranci teburin inda darajar kasuwarsa ta karu zuwa N789.6bn sai GT; N765.2bn, daga nan kuma sai First Bank mai N409.2bn, kamar yadda yazo a ranar Juma’a 31 ga Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a shekara 2

Kudaden da bankunan Najeriya suka tattara a 2021
Karshen 2021: Bankunan Najeriya mafi daraja da wadanda suka tafka asara a 2021 | Hoto: nairametrics.com
Asali: Facebook

Bangaren ma'aunin banki na NGX ya sami ribar 3.32% a cikin 2021, ya gaza isa zuwa ribar 10.14% da aka samu a shekarar da ta gabata, inji rahoton Nairametrics.

Sauran da ke cikin jerin sunayen sun hada da Access Bank da ke da N330.6bn, da UBA; N275.3bn, da Union Bank; N171.8bn, da kuma Fidelity Bank; N73.9bn.

Yadda lamarin yake dalla-dalla

A bankunan kasuwancin Najeriya 11 da ke kan gaba a NGX, First Bank ne ya yi nasara a wannan bitar yayin da bankin Sterling ya kasance babban mai asara ta fuskar kasuwanci.

First Bank a 2021 ya zarce irin su Access Bank da UBA inda suka tsaya a matsayi na 3 bayan samun 59.4% na hannun jari da ya rufa N11.4 kan kowacce kaso daga N7.15 da aka samu a karshen shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bashin da ake bin Najeriya ya kara mummunan tashi a 'yan watanni

Farashin kasuwar bankin First Bank ya samu N152.6bn a 2021 inda ya rufe kan N409.2bn na shekarar.

A nasa bangaren bankin Sterling shi ne ya fi yin asara a shekarar da ta gabata ta fuskar kaso, yayin da farashin hannun jarin sa ya ragu da 26% cikin 100%.

Ya kuma rufe shekarar kan kudi N43.5bn, yayin da GTCo ya yi asarar N186.9bn daga N952.1bn da aka samu a shekarar da ta gabata.

Wannan ne yasa bankin ya zama shi ne mafi tafka mummunan asarar 2021 da ta gabata.

A wani labarin, a watanni bakwai da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter, lamarin da ya kai tafka asarar NN546.5bn a lissafin da ya fito daga NetBlocks, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

A cewar kayan lissafin, Najeriya na tafka asarar N103.17m (kimanin dala 250,600) a duk sa'a a fannin tattalin arziki bisa dakatar da Twitter.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da shafin na Twitter a ranar Asabar 5 ga watan Yuni, 2021, haramcin ya tsaya ne bayan shafe kwanaki 222, wato sa'o'i 5328 kafin a dage shi a ranar Alhamis 12 ga watan Janairun 2022.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel