Yanzu-Yanzu: Sakataren Watsa Labarai na PDP ya yanke jiki ya faɗi a kotu

Yanzu-Yanzu: Sakataren Watsa Labarai na PDP ya yanke jiki ya faɗi a kotu

  • Chika Nwoba, Sakataren Watsa Labarai na Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen Jihar Ebonyi ya yanke jiki ya fadi a kotu
  • Tun ranar Lahadi ne jami'an tsaro na Ebubeagu suka kama shi suka mika shi hannun yan sanda bisa zarginsa da watsa labaran karya a dandalin sada zumunta.
  • Jam'iyyar PDP reshen Jihar Ebonyi ta yi ikirarin jami'an tsaro na Ebubeagu sun yi wa Nwoba duka kafin su mika shi hannun yan sanda

Jihar Ebonyi - Sakataren watsa labarai na jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Jihar Ebonyi, Chika Nwoba, ya yanke jiki ya fadi a kotu, The Nation ta ruwaito.

Nwoba ya fadi ne misalin karfe 3 na rana a lokacin da yan sanda suka kawo shi kotun Majistare ta 3 da ke Hedkwatar Shari'a a Abakaliki a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood

Yanzu-Yanzu: Sakataren Watsa Labarai na PDP ya yanke jiki ya faɗi a kotu
Sakataren Watsa Labarai na Jam'iyyar PDP ya yanke jiki ya fadi a kotu a Ebonyi. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kasance a hannun yan sanda tun ranar Lahadi a lokacin da jami'an tsaro na Ebubeagu suka mika shi bayan sun kama shi.

Ana zarginsa ne da watsa labarai na bogi a kafafen sada zumunta, laifin da aka tanadar wa hukunci karkashin doka ta 'laifukan yanar gizo' da gwamnati ta saka hannu a kai a shekarar 2021.

PDP ta yi ikirarin an lakada masa duka

Jam'iyyar PDP a Jihar ta Ebonyi ta yi ikirarin cewa jami'an tsaro na Ebubeagu da suka kama shi sun lakada masa duka kafin su mika shi hannun yan sanda a tsare shi.

Yan sandan ba su gurfanar da shi ba a ranar Talata duk da cewa an kawo shi harabar kotun.

Lauyansa, a ranar Talata, ya koka cewa yan sandan sun ki bari likitoci su duba shi duk da raunin da ya samu yayin dukar da aka masa.

Kara karanta wannan

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

Da aka kawo shi kotu a ranar Laraba, ya yanke jiki ya fadi a yayin da ya ke kokarin shiga kotun.

An yi kokarin farfado da shi amma hakan bai yiwu ba, daga nan aka garzaya da shi asibiti.

Daga bisani an dawo da shi kotun domin a gurfanar da shi

Amma, a yayin da yan jarida suke shirin barin wurin domin hada rahotanninsu, sun ga yan sanda sun dawo da shi.

A lokacin hada wannan rahoton, yana nan cikin mota a sharbe cikin rana.

Lauyansa. Luke Nkwegu ya shaidawa manema labarai cewa yan sandan sun bada umurnin a dawo da shi kotu a gurfanar da shi ko yana da rai ko ya mutu.

An gano cewa kotun tana jiran alkali ne ya iso kafin a gurfanar da shi.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fostan Ali Jita na takarar kujerar gwamnan Kano ya fara yawo a shafin soshiyal midiya

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel