Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

  • Hotunan wata kyanwa mai son maigidanta sun bazu a kafafen sada zumunta kuma mutane sun tofa albarkatun bakinsu
  • Sama da watanni biyu bayan mutuwar maigidanta, ta ki tashi daga kan kabarinsa saboda tsananin kewa
  • Mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan halin da kyanwan ke ciki kuma ko tana cin abinci

Wani mutumi mai suna @LavBosniak a kafar sada zumunta ya bayyana yadda wata kyanwa taki barin kan kabarin maigidanta bayan watanni da mutuwarsa.

@LavBosniak ya laburta wannan ne ranar Talata, 9 ga Nuwamba, 2021.

Ya ce mamacin mai suna Mufti Muamer Zukorlić ya mutu ya lokacin rani amma har aka fara sanyi kyanwar ta ki rabuwa da shi.

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa
Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa Hoto: @lavBosniak
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

Soyayya har bayan mutuwarsa

Hotunan sun nuna yadda kyanwar ke tsaye kan kabarin a zaune.

Mutane da dama sun bayyana cewa so da dama dabbobin da mutum ke kula da su da kyau sun fi son sa fiye da iyalansa da 'yayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel