Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood

Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood

  • Da alamun Kadaria Ahmed zata koma harkar fim don cin abinci yayinda ta bayyana shiga Nollywood
  • Kadaria ta kasance mace yar jaridar da tafi shahara a cikin mata yan jaridan Najeriya
  • Ta shahara da shirya muhawara da tattaunawa da yan takaran kujeran shugaban kasa yayinda ake shirin zabe

Shahrarriyar yar jaridar Najeriya, Kadaria Ahmed ta shiga duniyar kamfanin fina-finan Nollywood.

Kadaria Ahmed, yar asalin jihar Zamfara ta sanar da shigarta wani Fim na Nollywood a shafinta na Facebook.

Hakazalika ta saki hotunan Fim din da zata fito tare da jaruma Rahama Sadau.

Kalli wasu daga cikin hotunan da ta saki:

Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood
Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood Hoto: Kadaria Ahmed
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood
Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood Hoto: Kadaria Ahmed
Asali: Facebook

Kadaria Ahmad ta shahara da shirya muhawara da tattaunawa da yan takaran kujeran shugaban kasa yayinda ake shirin zabe.

A 2011, ta jagoranci muhawarar yan takara tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na CPC, Malam Ibrahim Shekarau na ANPP da Malam Nuhu Ribadu na ACN.

A 2019, ta sake shirya tattauna da dukkan yan takaran tare da mataimakansu a shirin 'The Interview' da gidanniyar McAuthur ta dau nauyi a tashar talabijin na NTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel