Da Dumi-Dumi: Masu Nadin sarauta sun sanar da sabon Sarkin Ibadan

Da Dumi-Dumi: Masu Nadin sarauta sun sanar da sabon Sarkin Ibadan

  • Duk yanayin dar-dar da ake ciki, majalisar naɗa sarki ta sanar da sabon Sarkin Ibadanland wanda ake kira 'Olubadan'
  • Mambobin majalisar 10 cikin 11 sun amince da Dakta Lekan Balogun, a matsayin sabon Olubadan na masarautar Ibadanland
  • Rahoto ya nuna cewa baki ɗaya mambobin majalisar sun samu halartan taron banda tsohon gwamna, Rashidi Ladoja

Ibadan, Oyo - Mutum 10 daga cikin mambobi 11 na majalisar zaben sarkin Ibadan wanda ake kira Olubadan, sun zaɓi Dakta Lekan Balogun, a matsayin sabon Olubadan na masarautar IbadanLand.

The Nation ta rahoto cewa majalisar zaben sabon sarki mai daraja ta farko ta musanta jita-jitar cewa rikici ka iya barkewa a wurin zaben sabon Basaraken.

Osi Balogun na masarautar Ibadanland, Chief Tajudeen Ajibola, shine ya bayyana haka a taron manema labarai da majalisar naɗa sarki ta kira ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu: An harbe 2, an sace 'yan China 3 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari wurin aikin lankarki na Zungeru

Lekan Balogun
Da Dumi-Dumi: Masu Nadin sarauta sun sanar da sabon Sarkin Ibadan Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar Ajibola, majalisar ta cimma matsayar cewa Dakta Balogun, shi ne na gaba a layi da zai gaji sarautar Olubadan kamar yadda al'adar masarautar ta tanada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin dagaske ne sabon sarkin ba shi da lafiya?

Haka nan kuma, ya yi watsi da jita-jitar da mutane ke yaɗa wa cewa sabon Basaraken ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai jagoranci al'umma.

Ajibola ya ƙara da cewa duk wasu rahotanni marasa kyau da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba wasu abun damuwa bane.

Taron yan majalisar zaben sabon basaraken ya samu halartan dukkan mambobi ban da tsohon gwamna Rashidi Ladoja.

Mambobin majalisa da suka halarci taron

Wadan da suka samu halartan taron sun haɗa da, Balogun Olubadan, Owolabi Olakulehin; Otun Balogun, Olufemi Olaifa; Ashipa Olubadan, Eddy Oyewole; da kuma Osi Balogun, Tajudeen Ajibola.

Kara karanta wannan

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

Sauran sun haɗa da, Ekaarun Olubadan, Amidu Ajibade; Ashila Balogun Olubadan, Lateef Gbadamosi; Ekaarun Balogun, Kola Adegbola da kuma Ekerin Olubadan Abiodun Kola-Daisi.

Ana tsammanin sabon sarkin da aka zaba zai yi jawabi ga mutane a wurin taron na ranar Laraba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A wani labarin kuma Gwamnan APC ya rantsar da sabbin ciyamomi 35 da mutane suka zaba a jiharsa

Gwamna Kayode Fayemi na jam'iyyar APC ya rantsar tare da jan hankalin sabbin ciyamomi 35 da mutane suka zaba a jihar Ekiti.

Fayemi ya roki sabbin shugabannin su saka aikin al'umma, walwala da jin daɗin su da kuma tsaro a kan gaba fiye da abin da ransu ke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel