Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

  • Gagarumin kantin saide-saide da ke Kado a babban birnin tarayya na Abuja mai suna Next Cash and Carry, ya kama da wuta
  • A halin yanzu, motoci uku ke farfajiyar kantin suna kokarin kashe mummunar gobarar da ba san abinda ya tada ta ba
  • Har a halin yanzu, ba a san ko gobarar ta ci rai ba duk da yadda ta ke ta balbali tare da lamushe dukiyoyi

Kado, Abuja - Fitaccen katafaren kantin Next Cash and Carry da ke Kado a babban birnin tarayya na Abuja ya na ci da wuta.

Har a halin yanzu dai, ba a gano abinda ya kawo mummunan gobarar ba yayin da Daily Trust ta ziyarci wurin da lamarin ke faruwa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja na ci da wuta
Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja na ci da wuta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A inda lamarin ke faruwa, an ga masu kashe gobara suna kokarin kashewa. A kalla motoci uku na kashe wuta aka gani a farfajiyar kantin.

Ba a tabbatar ko gobarar ta ci rai ba har yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na nan tafe...

y

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel