Tuna baya: A 2013, Musulma 'yar Najeriya ta ci gasar sarauniyar kyau ta duniya

Tuna baya: A 2013, Musulma 'yar Najeriya ta ci gasar sarauniyar kyau ta duniya

  • Obabiyi Aishah Ajibola, sarauniyar kyawun Najeriya, ta lashe gasar sarauniyar kyau musulma ta duniya a Jakarta kasar Indonesia a ranar 18 ga watan Satumban 2013
  • Gasar wacce gidauniyar musulmai ta duniya ta shirya, ta janyo zanga-zanga da cece-kuce daga bangarori daban-daban na duniya
  • Kamar yadda a lokacin bayanai su ka nuna, ‘yar Najeriyan mai shekaru 21 ta lashe gasar ne ba don kyau kadai ba har da ilimin addininta da na Qur’ani

Obabiyi Aishah Ajibola, ‘yar Najeriya ce da ta lashe gasar kyau na musulman duniya wacce aka yi a Jakarta kasar Indonesia a ranar 18 ga watan Satumban 2013.

Gasar wacce gidauniyar musulmai ta shirya a Bali da ke Indonesia a ranar 28 ga watan Satumban 2018 ta janyo cece kuce iri-iri a lokacin, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shatu Garko: Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah

Duk da dai gasar wacce ‘yar Najeriyar mai shekaru 21 ta lashe ba don kyau kadai bane har da ilimin iya karatun Qur’ani mai girma tare da sauran ilimomi akan addinin musulunci.

Tuna baya: A 2013, Musulma 'yar Najeriya ta ci gasar sarauniyar kyau ta duniya
Tuna baya: A 2013, Musulma 'yar Najeriya ta ci gasar sarauniyar kyau ta duniya. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Fiye da mata 500 sun shiga gasar kuma sun yi kokarin amsa tambayoyin ta yanar gizo dangane da sanin su akan musulunci, ciki har da lokacin da su ka fara amfani da hijabi wanda hakan na daya daga cikin abinda ake dubawa a gasar kyawun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane 20 ne su ka yi karkon zama zakakurai daga kasashe daban-daban, har da Najeriya, Brunei, Bangladesh, Iran, Malaysia da Indonesia na gasar ta musulunci wacce malamai da dama su ka soka, TheCable ta ruwaito.

Wadanda su ka shirya gasar sun bayyana cewa suna so ne su nuna wa mata musulmai cewa akwai wata hanyar bayyana kyau kuma sun kai shiga gasar kyauwun duniya.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

A wannan shekarar, karo na 12 da suka yi gasar, gasar da musulman duniya ta zama ta mata zalla. Kuma ba su amince da amfani da dan kamfai da rigar mama kadai ba a matsayin daya daga cikin sutturar da za a sa wurin gasar.

Yayin da Ajibola ta lashe gasar a shekarar 2013, ta tafi da kyautar rupee miliyan 25 (£1,375) da kuma damar kai ziyara Makkah da kasar Indiya.

Bayan shekaru 8 ne Shatu Garko, wata ‘yar kwalisa daga jihar Kano ta dauki hankalin jama’a bayan ta zama mace ta farko da ta lashe gasar kyau a Najeriya mai sanya hijabi tsawon shekaru 64 da aka fara gasar.

An ruwaito yadda Garko tace:

“Lashe gasar nan babbar nasara ce a rayuwata. Ni dai ina fatan zama sarauniyar kyau ta Najeriya. Ina godiya ga wadanda su ka sa gasar da masu daukar nauyin ta.
“Ina godiya ga mahaifiyata akan kaunar da ta nuna min.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

Sai dai kwamandan Hisbah na jihar Kano, Haruna Ibn-Sina ya ce haramun ne shigar Garko wannan gasar.

Ya ce gasar ta ci karo da koyarwar addinin islama don haka har iyayenta zai gayyata don su amsa tambayoyi.

Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko

A wani labari na daban, Shatu Garko, Sarauniyar kyau ta 44 a Najeriya ta shaida yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.

Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta kashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaida wa The Punch a wata hira da jaridar ta yi da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel