Duk dan siyasar da ya ki cika muku alkawari kuyi masa jifan shaidan, inji dan majalisa

Duk dan siyasar da ya ki cika muku alkawari kuyi masa jifan shaidan, inji dan majalisa

  • Dan majalisar tarayya daga jihar Edo ya bayyana abin da ya kamata a yi wa duk dan siyarar da bai iya tabuka komai ba
  • Dan siyasar ya ce, duk dan siyasar da ya gagara tabuka wani abu ya kamata mutane su jefe shi kawai
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake rabawa mutanen mazabarsa babura, inda ya bayyana irin shirinsa na siyasa

Edo - Dennis Idahosa, dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Ovia, ya bukaci mazauna jihar Edo da su jefi ‘yan siyasar da suka yi watsi da alkawuran da suka dauka a yakin neman zabe.

Idahosa ya yi magana ne a lokacin da ya raba babura ga mata da matasa 160 a Iguobazuwa, Ovia, kudu maso yammacin karamar hukumar Edo, ranar Asabar, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari

Ya ce bisa tsarin da aka gindaya a mazabar, mutane ba za su lamunci duk dan siyasar da bai tabuka komai ba.

Dan siyasa ya rabawa 'yan mazabarsa babura
Duk dan siyasar da ya ki cika muku alkawari kuyi masa jifan shaidan, inji dan majalisa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Idahosa, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan bin doka da oda, ya ce baya ga shirin karfafawa, yana da ayyuka sama da 54 da aka kammala da kuma wadanda ke gudana a sassa 23 da suka kunshi mazabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta ruwaito shi yana cewa:

“Ba batun cin zabe ba ne, batun cika alkawuran yakin neman zabe. Har ila yau, muna cika wani bangare na alkawurran da muka yi a yakin neman zabe.
“Wannan alkawari na ne kawai ga al’ummar mazabar tarayya ta Ovia, haka kuma na yi hakan saboda Allah dan kuma na canza labaran da suka faru a baya."
"A lokacin da muka gama, duk wanda zai zo dole ne ya yi aiki, ko kuma a jefe shi."

Kara karanta wannan

Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

Sunday Aghedo, zababben dan majalisar dokokin jihar, ya bayyana Idahosa a matsayin wakili mai inganci na mazabar tarayya ta Ovia.

A cewar Sunday:

"Akwai wasu kafinshi, amma sun kasa yin abin da Idahosa ke yi a yanzu. Ya kafa ma’auni da masu zuwa a bayansa za su yi kokarin cimmawa.
"Abin da yake yi a yau ba a taba yin irinsa ba a tarihin mazabar tarayya ta Ovia."

A nasa bangaren, sakataren jam’iyyar APC a jihar Lawrence Okah, ya bukaci wadanda suka amfana a shirin da su kula da baburan yadda ya kamata.

A cewarsa:

"Wadannan babura za su ba ku damar yin aiki tare da kula da iyalan ku."

Bidiyon sanatan Najeriya yayin da yake aikin sarrafa cunkoson ababen hawa a Abuja

A wani labarin, sanatan Najeriya ya canja sana’a na wasu ‘yan mintoci yayin da ya zama jami'i mai kula da zirga-zirgar ababen hawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon sanatan Najeriya yayin da yake aikin sarrafa cunkoson ababen hawa a Abuja

Sanatan na Borno ta Kudu mai suna Mohammed Ali Ndume an dauki bidiyonsa ne yayin da yake kokarin sassauta cunkoson ababen hawa a wata babbar hanya a Abuja.

Sanata Ndume ya nuna karimci yayin da yake gudanar da aikin sarrafa zirga-zirgar ababen inda yake sanye da babbar riga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel