Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari

Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari

  • Gwamna Aminu Masari na Katsina ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya daga Abuja
  • Gwamnan ya bayyana cewa ba'a dauki komai a gidan ba kuma babu alamun balle kofa
  • Ya ce da sannu bincike zai bayyana ainihin abinda ya faru da kuma wanda ya kashe Kwamishanan

Kastina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa kisan Kwamishanan Kimiya da Fasahar jihar da akayi da lauje cikin nadi.

Masari yace duk da matsalar tsaro da annobar yan bindiga masu garkuwa da mutane, yadda aka kashe Dakta Rabe daban ne.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo ziyarar jaje, rahoton DailyTrust.

Gwamnan yace ba'a dauki komai a gidan ba kuma ba'ayi garkuwa da kowa ba. Ko balla kofa ba'a yi ba, yace.

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

Yace:

"Ba da bindiga aka kasheshi ba, da wuka aka kashe shi, ba'a sace komai na shi ba. Kuma ba'a balla gidan ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jana'iza Gwamna Masari
Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamnan yace mutum biyu ke iya kashe Kwamishanan, wanda ke tare da mamacin ko kuma dan gidan.

A cewarsa:

"Kamar yadda na fada, abinda mutum zai fahimta shine, duk wanda ya aikata wannan abin toh mamacin ya bashi daman shiga dakin, ko kuma wanda ke da mukullan shiga dakinsa."
"Amma na san binciken jami'an tsaro zai bayyana abinda ya faru."

An yi jana'izar Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina da aka kashe a gidansa

An gudanar Sallar Jana'izarsa karkashin jagorancin Limamin Masallacin Katsina GRA, Dr Aminu Abdullahi Yammawa.

An bizne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana'izar, rahoto DailyTrust.

Wadanda suka halarci Jana'izar sun hada da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello MAsari da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai bada shawara kan lamuran tsaro, Manjo Janar Babagna Monguno.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina, Majiya

Sauran sune Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Nasir; Shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufa’I Abubakar da MAnjo Janar Samuel Adebayo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel