Kano: Ganduje ya miƙa mulki ga mataimakinsa Gawuna, ya tafi Jami'ar Harvard

Kano: Ganduje ya miƙa mulki ga mataimakinsa Gawuna, ya tafi Jami'ar Harvard

  • Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa Nasiru Gawuna
  • Ganduje ya yi hakan ne yayin da zai tafi Jami'ar Harvard ta Amurka domin hallartar wani taron shugabanci na mako daya
  • Muhammad Garba, Kwamishinan labarai na jihar Kano ne ya bada sanarwar yana mai cewa a yanzu mataimakin gwamnan yana da cikakken iko

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tafi kasar Amurka domin hallartar wani taro na sati guda a Jami'ar Harvard, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar da kwamishinan Labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar ta ce Mr Ganduje zai hallarci taron 'Cigaban Jagoranci na Ainihi' a Tsangayar Koyar Dabarun Kasuwanci ta Harvard da ke Boston.

Kano: Ganduje ya mika mulki ga mataimakinsa, ya shilla zuwa Harvard
Gwamnan Kano Ganduje ya mika mulki ga mataimakinsa Gawuna, ta kama hanyar zuwa Harvard. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Gawuna na da cikakken iko har zuwa lokacin da Ganduje zai dawo

Kara karanta wannan

Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

Ya ce gwamnan ya mika mulki tare da cikakken iko ga mataimakin gwamna, Nasir Gawuna, ya yi aiki a matsayin gwamna na wucin gadi a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa daga yanzu za a rika tura duk wasu ayyuka na gwamnati zuwa ofishin mataimakin gwamnan domin ya dauki matakin da ya dace a kansu.

Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

A wani labarin, kotun daukaka kara ta sa rabar 16 ga watan Disamban 2021 ta zama ranar sauraron kara don sanin matsaya daga hukunci da babbar kotun FCT wacce ta wofantar da gangamin gundumar Kano na APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta ce mambobin kwamitin shirya gangami ne su ka daukaka karar gaban kotun da ke Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin cikin gida zai kawo masa cikas a Kano, Tinubu zai zauna da Gwamna Ganduje

A wata takarda wacce kwamishinan labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya saki a ranar Talata, ya ce APC tana jiran jin hukuncin kotun don sanin matakin gaba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel