Ku kara kaimi wajen ragargazan yan tada kayar baya cikin kankanin lokaci, Shugaba Buhari ga Sojoji

Ku kara kaimi wajen ragargazan yan tada kayar baya cikin kankanin lokaci, Shugaba Buhari ga Sojoji

  • Shugaba Buhari ya yi kira ga dakarun rundunar sojin kasar nan su nunka kokarin su wajen kawo karshen ayyukan tada kayar baya
  • Buhari yace sojojin na samun nasara sosai a yankin arewa maso gabas, amma duk da haka akwai babban aiki a gaban su
  • Ya kuma bukaci sojojin su rinka aiki suna kula da dokoki da ka'idojin kare hakkin bil'adama

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci sojojin Najeriya su kara kaimi wajen tattara bayanan fasaha domin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

Da yake jawabi ranar Litinin a wurin bude taron hafsan rundunar sojin ƙasa (COAS) 2021, Buhari yace yaƙi da yan ta'adda da masu tada ƙayar baya na bukatar fasaha, "Tattara bayanai da kuma ɗaukar mataki akai."

The Cable ta rahoto cewa Shugaban ƙasa wanda ya samu wakilcin shugaban jami'an tsaro, Lucky Iraboh, yace gwamnati na cigaba da tattauna wa da kawayenta ƙasashe domin samar da kayan aiki ga sojoji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata gudanar da bincike kan mummunan kisan da akai wa Fulani a jihar Edo

Shugaba Buhari
Ku kara kaimi wajen ragargazan yan tada kayar baya cikin kankanin lokaci, Shugaba Buhari ga Sojoji Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Tribune ta rahoto Buhari yace:

"Lamarin yana bukatar haɗin kan hukumomin tsaro. Saboda haka ina kira da ku kara kaimi wajen tattara bayanai da kuma haɗa kai wajen aikin gano bayanan fasaha domin ku lallasa ta'addanci da tada kayar baya a kasar nan cikin lokaci kankani."
"Ina sane da nasarorin da kuka samu zuwa yanzu a arewa maso gabas, wanda ya jawo mika wuyan wasu daga cikin yan ta'addan cikin watannin da suka gabata."
"Dan haka ya zama wajibi ku rike wannan nasaran domin tabbatar da yan ta'addan sun cigaba da aje makamansu, har zaman lafiya ya dawo a yankin."

Ku kara zage dantse a filin daga - Buhari

Bayan haka, shugaba Buhari ya roki dakarun sojin su cigaba da nuna kwarewarsu wajen kare demokaradiyya da kuma dakile harin yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Ya kuma roki kwamandojin soji su kula da jami'an dake ƙarƙashinsu yanda ya kamata, da kayan aiki domin samun sakamako mai kyau a filin yaki.

"Saboda haka kasancewarku dakarun sojin kasar mu, aikin ku na samar da tsaro ga kasa yana da matukar muhimmanci."
"Yayin da kuke kokarin sauke nauyin dake kan ku, ina rokon ku sa basira, sannan ku cigaba da aiki kan tsarin dokoki da ƙa'idojin kare hakkin bil adama."

A wani labarin kuma Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi, sun kone matafiya da ransu

Yan ta'adda sun kai wani mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara, sun sace mutane da dama.

Rahoto ya nuna cewa yan bindigan karkashin jagorancin Turji, sun mamaye hanyar, inda suka kashe mutane 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel