Da yiwuwan Gwamnatin Sin ta kwace tashar jirgin saman Uganda saboda gaza biya basussukan da ake binta

Da yiwuwan Gwamnatin Sin ta kwace tashar jirgin saman Uganda saboda gaza biya basussukan da ake binta

  • Gwamnatin Uganda na nadamar amincewa da wasu sharudda yayinda ta karbi bashi hannun kasar Sin a 2015
  • A yarjejniyar, Gwamnatin Uganda ta amince a kwace tashar jirgin samanta babba idan ta gaza biyan kudin
  • Yanzu Gwamnatin ta garzaya birnin tarayyar China don neman alfarma janye wannan sharadi

Gwamnatin kasar Uganda na gab da rashin babbar tashar jirgin samanta na kasa da kasa sakamakon gaza biyan bashin da ta karba hannun Gwamnatin kasar Sin.

Tashar jirgin saman mai suna Entebbe International na cikin dukiyoyin da Gwamnatin Uganda ta sanya cikin sharadi yayinda ta karbi bashi hannun China kuma ta amince a kwace tashar idan ta gaza biya.

A cewar rahotanni, Shugaban kasar, Yoweri Museveni, ya tura tawaga birnin Beijing don neman sauki wajen yarjejeniyar.

Amma wannan tawaga bata samu nasara ba inda Gwamnatin Sin tace sam ba za'a canza komai cikin yarjejeniyar ba.

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

A ranar 17 ga Nuwamba, 2015, Ma'aikatar kudi da Sufurin Uganda ta rattafa hannu kan yarjejeniya da bankin shige da fice na kasar China don karban bashin U$207 million da sharadin kudin ruwa na 2%; kuma zasu iya biya cikin shekaru 20, da kuma yiwuwan talalan shekaru 7.

A yarjejeniyar, Uganda ta bada daman a kwace tashar jirginta.

Kin amincewar Gwamnatin Sin na sake tattaunawa kan lamarin ya jefa gwamnatin Musevini cikin rudani.

Gwamnatin Sin ta kwace tashar jirgin saman Uganda
Da yiwuwan Gwamnatin Sin ta kwace tashar jirgin saman Uganda saboda gaza biya basussukan da ake binta
Asali: Facebook

A cewar Daily Monitor, Gwamnatin Uganda ta amince da soke dukkan hakkokinta don karban basussukan kudade.

A makon da ya gabata, Ministan kudin Uganda, Matia Kasaija, ya baiwa yan majalisa hakuri bisa rattafa hannu kan wannan yarjejeniya.

Yace:

"Ina bada hakuri cewa bai kamata ace mun amince da wannan sharruda."

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Bayan haka, yan majalisan sun yi tsokaci kan adadin kudin ruwan da bankin Sin ta sanya kan kudin da Uganda tayi amfani da su matsayin jingina.

Ka daina cin bashi daga Kasar Sin – IMF ta fadawa Buhari

A shekarar 2019, mun kawo muku labari cewa manyan kungiyoyin harkar tattalin arziki na Duniya sun ja kunnen Najeriya game da cin bashi a wasu kasashen. Kungiyar IMF mai bada lamuni ta Duniya ita ce wanda ta fito tayi irin wannan magana kwanan nan.

Kungiyar ta nemi Najeriya da sauran kasashe su rika bi a hankali wajen karbar aron kudi daga ketare. IMF ta nemi irin su Najeriya da su rika duba ka'idojin da ake maka masu yayin da su ke neman cin bashi daga kasashen waje.

Wani babban jami’i kungiyar da ke bada lamuni ga kasashen Duniya watau IMF ya fito ya shawarci kasashen Najeriya da sauran Takwaorin ta masu tasowa da su kara yawan harajin da su ke karba a cikin gida wanda ake kira VAT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel