Ka daina cin bashi daga Kasar Sin – IMF ta fadawa Buhari

Ka daina cin bashi daga Kasar Sin – IMF ta fadawa Buhari

Mun samu labari cewa manyan kungiyoyin harkar tattalin arziki na Duniya sun ja kunnen Najeriya game da cin bashi a wasu kasashen. Kungiyar IMF mai bada lamuni ta Duniya ita ce wanda ta fito tayi irin wannan magana kwanan nan.

Kungiyar ta nemi Najeriya da sauran kasashe su rika bi a hankali wajen karbar aron kudi daga ketare. IMF ta nemi irin su Najeriya da su rika duba ka'idojin da ake maka masu yayin da su ke neman cin bashi daga kasashen waje.

Wani babban jami’i kungiyar da ke bada lamuni ga kasashen Duniya watau IMF ya fito ya shawarci kasashen Najeriya da sauran Takwaorin ta masu tasowa da su kara yawan harajin da su ke karba a cikin gida wanda ake kira VAT

KU KARANTA: PDP ta na so a binciki Buhari a kan bashin kudin da ke kan Najeriya

Ka daina cin bashi daga Kasar Sin – IMF ta fadawa Buhari
IMF ta na so a kara haraji sannan a kara himma a gidan kwastam
Asali: UGC

Tobias Adrian yake cewa akwai bukatar Najeriya ta kuma dage wajen samun kudin shiga ta hanyar gidan kwastam. Tobias Adrian yayi wannan bayani ne a Ranar Laraba 10 ga Watan Afrilu. Adrian yace Najeriya na yawan cin bashi daga Sin.

Wannan babban jami’in na IMF ya kuma bayyana cewa Najeriya ita ce kasar da ba ta kashe kudin da ke cikin babban asusun ta na sovereign wealth fund yadda ya kamata. Mista Adrian ya fadi wannan ne wajen taron IMF da bankin Duniya.

IMF ta nuna cewa babu wata matsala game da cin bashi daga kasar Sin, sai dai tace ya kamata kasashen da ake aro kudi su rika lura da sharudodin da ake gindaya masu, ka da su jefa kan su a sarkakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel