'Yan sanda sun ceto dalibai 5 da wasu mutum 19 da 'yan bindiga suka sace a Zamfara
- Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa dasu a wasu yankunan jihar
- An ceto wasu dalibai da aka sace a jihar, watau daga cikinsu dalibai ne da aka sace a hanyarsu ta dawowa daga rubuta jarabawar WAEC
- Tuni aka mika su ga gwamnatin jihar Zamfara, inda ta bayyana cewa, za ta tabbatar da tsaro a makarantu a jihar
Zamfara - Hukumomin ‘yan sanda a Zamfara sun ce sun ceto mutane 24 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Shinkafi da Tsafe na jihar, Channels Tv ta ruwaito.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa daga cikin wadanda jami’an tsaro suka ceto akwai dalibai biyar, ciki har da dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Kaura Namoda.
Elkana ya bayyana sauran dalibai hudun a matsayin daliban makarantar Sakandare ta gwamnati ta Birnin Yero a karamar hukumar Shinkafi, wadanda aka sace a hanyarsu ta dawowa daga rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC.
A cewarsa, jami’an ‘yan sanda sun ceto mutanen da aka sacen ne daga wurare daban-daban a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa jami’an da aka tura hanyar Gusau Tsafe zuwa Funtua sun ceto fasinjoji 11 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin da suke tafiya cikin dare a cikin motoci biyu.
Ya gargadi masu ababen hawa da su daina shiga jihar da daddare, yana mai cewa umarnin gwamnatin jihar na takaita zirga-zirgar fasinjoji a ciki da wajen jihar cikin dare ya rage sace-sace.
The Street Journal ta ruwaito shi yana cewa:
"Wadanda abin ya shafa, wadanda suka shafe kwanaki 60 a hannunsu, yanzu an ceto su ba tare da wani sharadi ba."
Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya karbi wadanda aka sace daga hannun ‘yan sanda a madadin gwamnatin jihar.
Dosara ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da tsaro a kewayen makarantu domin kare daliban jihar.
'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas
A wani labarin, an kashe wani malamin jami'a mai suna Ahmed Saheed da dalibin digiri dan aji daya a Kwalejin Ilimin Kiwon Lafiya ta Farko ta Michael Otedola (MOCPED) da ke karamar Hukumar Epe a Jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.
An ce an kashe malamin ne a kusa da garin Poka da ke Epe, yayin da dalibin mai suna Razak Bakare kuma aka harbe shi a harabar jami’ar.
Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Daily Trust cewa, lamurran masu ban takaici, sun faru ne cikin sa’o’i 48.
Asali: Legit.ng