Gwarazan yan sanda sun ceto matafiyan da yan bindiga suka sace a hanyar Kaduna-Abuja, Mutum daya ya mutu

Gwarazan yan sanda sun ceto matafiyan da yan bindiga suka sace a hanyar Kaduna-Abuja, Mutum daya ya mutu

  • kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Abdullahi Mudassiru, ya bayyana cewa yan sanda sun ceto matafiya 11 da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja
  • Kwamishinan yace yan sanda sun gano motar mutum ɗaya da ya mutu a harin, Alhaji Muhammadu Hamidu
  • Gwamnatin Kaduna tace zata cigaba da bibiyar halin da ake ciki yayin da jami'an tsaro ke kokarin ceto sauran

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun kai mata bayani kan halin da ake ciki biyo bayan harin da aka kai hanyar Kaduna- Abuja.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.

Kwamishinan yan sanda, Abdullahi Mudassiru, da kwamandan rundunar soji ta One Division, sune suka jagoranci sauran hukumomin tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Shugaba Buhari, sun kashe mutane da dama

Jami'an tsaro
Gwarazan yan sanda sun ceto matafiyan da yan bindiga suka sace a hanyar Kaduna-Abuja, Mutum daya ya mutu Hoto: Ministry of Internal Security
Asali: Facebook

Yan bindiga sun farmaki matafiyan ne a Kurmin Kare, dake karamar hukumar Kachia, inda suka bar gawar mutum ɗaya, tare da sace adadi mai yawa na mutane.

Yan sanda sun ceto mutum 11

Kwamishinan yan sandan ya bayyana cewa jami'ai sun kubutar da mutum 11 daga hannun maharan, yayin da wani mutun ɗaya, Alhaji Muhammad Sagir Hamidu, ya rasa rayuwarsa.

Ya bayyana cewa jami'an sun gano motar hawan Alhaji Hamidu, wanda shine shugaban makarantar Famaks British.

Wane mataki hukumomin tsaro ke ɗauka?

Dangane da matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka, Kwamishinan ya kara da cewa tuni hukumar yan sanda ta jibge jami'anta a kan hanyar.

Ya kuma bayyana cewa kokarin da jami'an yan sanda ke cigaba da yi na ceto sauran matafiya, yana samun tallafin sojoji.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsagerun yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar gwamna a hanyar Abuja-Kaduna

A nashi ɓangaren kwamandan rundunar soji ta Division One, ya bayyana wa gwamnatin Kaduna irin matakan da sojoji suke ɗauka.

Ya tabbatar wa gwamnatin cewa tuni suka jibge haɗakar jami'an tsaro a wurare da dama, kuma yanzun haka suna cigaba da aikin bincike.

Me gwamnatin Kaduna tace?

Da yake martani, kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, yace gwamnatin Kaduna, zata cigaba da bibiyar halin da ake ciki kan lamarin.

Kazalika ya sake jaddada kokarin gwamnati na tallafawa hukumomin tsaro da kayan aiki, kuma ya kura harin da babban ci baya.

A wani labarin kuma Mutum 5 sun kone kurmus yayin da tanka makare da mai ta fashe a Ibadan-Legas

Wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar fashewar Tankar dakon mai ya lakume rayukan akalla mutun 5.

Rahoto ya bayyana cewa Tanka makare da man fetur ta yi taho mu gama da wata babbar mota a hanyar Ibadan-Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel