Na zuba makudan kudi don farfado da tattalin arziki da inganta rayukan yan Najeriya: Buhari

Na zuba makudan kudi don farfado da tattalin arziki da inganta rayukan yan Najeriya: Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana irin makudan kudaden da ya shirya kashewa don inganta rayukan yan Najeriya
  • Buhari ya bayyanawa manyan yan kasuwa a Faransa cewa gwamnatinsa ta shirya tsari na samar da tsaro
  • Shugaban kasan yace ana zuba kudi wajen gine-gine domin janyo hankalin yan kasuwa masu zuba jari

Paris - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta farfado da tattalin arzikin Najeriya, ya gina manyan ayyuka da kuma inganta jindadin yan Najeriiya.

Buhari ya bayyana hakan ne ga masu zuba hannun jari a kasar Faransa ranar Laraba yayin taron hadin kai tsakanin Najeriya da yan kasashen waje.

Shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta zuba makudan kudi wajen ilmantar da mutane, kara ingancin asibitoci, manya ayyuka, karfafa mata yakar sauyin yanayi da samar da abinci.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

"Yau wadannan ayyuka da muka yi na baiwa mutane daman samawa kansu aiki, kara yawan ma'aikata da kuma karfafa ilmin jama'a don cigaban kasa."
"Dubi ga muhimmacin tsaro ga kasa, mun sauya tsarin yaki da matsalar tsaron mu a 2019."
"Aiwatar da wannan tsarin ya taimaka matuka wajen nasarorin da muka samu wajen yaki da yan bindiga da yan ta'adda a Arewa maso gabashin Najeriya."

Na zuba makudan kudi don farfado da tattalin arziki
Na zuba makudan kudi don farfado da tattalin arziki da inganta rayukan yan Najeriya: Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Muna aiwatar da manyan ayyuka

Buhari yace gwamnatinsa na gudanar da manyan ayyuka a sassa da dama tun lokacin da ya hau mulki domin inganta rayukan yan Najeriya.

Yace:

"Jimillar kudi 1.5 trillion Dollars zamu kashe cikin shekaru goma daga 2015."
"Kawo yanzu, mun zuba makudan kudi wajen ginin layukan dogon jirgin kasa, tashohin ruwa, tituna, gidaje, da sauransu domin jan hankulan masu zuba hannun jari."

Kara karanta wannan

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Asali: Legit.ng

Online view pixel