Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa ya ƙaru a Kaduna sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi

Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa ya ƙaru a Kaduna sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnati ta yi

  • Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, reshen jihar Kaduna, Rabaran John Joseph Hayeph ya bayyana yadda ‘yan bindiga su ka kara yawan kudin fansa sakamakon yadda gwamnatin jihar Kaduna ta toshe hanyoyin sadarwa
  • Tun bayan gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin a wasu kananun hukumomi da ke jihar kamar yadda jihar Zamfara da Katsina su ka yi don kawo garanbawul akan matsalar tsaro, lamurra su ka canja
  • Har ila yau, wani Malam Abubukar, mai nazari akan sha’anonin rayuwa, ya ce ya kamata gwamnati ta dinga tuntubar mutane kafin ta dauki matakan tsaro don gudun barkewar matsaloli

Jihar Kaduna - Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, reshen jihar, Rabaran John Joseph Hayeph, ya bayyana yadda ‘yan bindiga su ka kara farashin kudin fansar jama’an da suka yi garkuwa da su.

Read also

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Kamar yadda VOA Hausa ta ruwaito, ya ce hakan ya biyo bayan datse kafofin sadarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ne.

Shugaban CAN: Farashin kuɗin fansa da ƴan bindiga suke amsa ya ƙaru bayan rufe kafafen sadarwa a Kaduna
Farashin kuɗin fansa da ƴan bindiga suke amsa ya ƙaru bayan rufe kafafen sadarwa a Kaduna, Shugaban CAN. Hoto: The Punch
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

VOA Hausa ta bayyana yadda kusan wata daya kenan da gwamnatin jihar Kaduna ta datse kafofin sadarwa kamar yadda jihar Zamfara da Katsina su ka yi don kawo gyara akan matsalolin tsaro.

Ba wannan kadai bane matakin tsaro da gwamnati ta dauka ba, ta hana yawo a babura, kuma ta dakatar da shige da fice a ababen hawan haya idan karfe 7 na yamma ya yi a jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kwashe watanni 3 ana bin wadannan sabbin dokokin da ta shimfida.

Shugaban CAN ya ce matakin be haifar da da mai ido ba

Sai dai shugaban CAN din ya ce matakin be haifi da mai ido ba, don kara tabarbare lamurra ya yi.

Read also

Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara

Malam Abubakar Aliyu, wani manazarcin harkokin rayuwa ya ce ya kamata kafin gwamnati ta dauki mataki akan tsaro ta fara tuntubar jama’a don jin ta bakin su.

A bangaren kwamishinan harkokin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya ce duk mai sukar wannan matakin ya na da wata manufa a siyasance.

A ranar Lahadin da ta gabata ‘yan bindiga su ka kai farmaki wata cocin Baptist da ke Kakau Daji inda su ka yi awon gaba da masu bauta bayan sun bude mu su wuta.

Shugaban kungiyar kiristoci reshen jihar Kaduna da kan shi ya tabbatar wa da manema labarai yadda lamarin ya auku.

An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa

A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.

Read also

Zamfara: Jerin kasuwanni 7 da Matawalle ya bada umurnin a buɗe su

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Source: Legit.ng

Online view pixel