Yan sanda sun kama abokan aikinsu suna ƙwacewa wani matafiyi kuɗi

Yan sanda sun kama abokan aikinsu suna ƙwacewa wani matafiyi kuɗi

  • ‘Yan sanda sun kama wasu jami’an su da kwacen kudi daga hannun wani matafiyi, Victor Aguwah
  • Hakan ya biyo bayan korafin da ya kai wa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Rabiu Hussaini
  • A cewarsa jami’in ya bukaci ya tura masa N60,000 ne ta POS kuma ya amshi kudin ne bisa tilastawa

Imo - Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu jami’in ta da laifin kwacen kudin daga hannun wani matafiyi, Victor Agunwah bayan ya kai korafi wurin Rabiu Hussaini, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo.

The Cable ta ruwaito yadda ya kai karar ne inda ya bayyana cewa dan sandan ya kwace N60,000 a wurin sa inda ya bukaci ya tura masa ta POS.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Hisbah sun kama Aliyu Na Idris da ke son sayar da kansa kan N20m domin talauci

Dara ta ci gida: Ƴan sanda sun kama abokan aikinsu ƴan sanda da suka tare matafiyi suka ƙwace masa kuɗi
'Yan sanda sun kama abokan aikinsu ƴan sanda da suka tare matafiyi suka ƙwace masa kuɗi. Hoto:The Cable
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa dan sandan ya cutar da shi da sauran wadanda su ke cikin motar inda ya tilasta ma sa tura ma sa kudin bisa ruwayar The Cable.

A takardar ta ranar Laraba, kwamishinan ‘yan sandan ya ce sun kama wanda ake zargin kuma yanzu haka ya na hedkwatar ‘yan sanda don fuskantar hukunci.

A cewar CP Hussaini mai laifin ya na fuskantar tuhuma a hannun hukuma. Sai dai be bayyana sunan jami’in ba.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

“Rundunar ‘yan sanda ta fara bincike akan wani rahoto da ya yita yawo akan wani jami’in ‘yan sanda wanda ya yi kwacen N60,000 daga wani Victor Aguwah, matafiyi daga hanyar filin jirgin Sam Mbakwe zuwa kauyen Mbaise.”

Kwamishinan ya nuna takaicin sa akan lamarin

Kwamishinan ya nuna rashin jin dadin sa akan lamarin inda ya ce an gano jami’in, an kama shi kuma ya na hannun ‘yan sandan bangaren binciken sirri na jihar (SCIID), don a hukunta shi.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana a takardar:

“Rundunar ta tuntubi wanda lamarin ya faru da shi ta wayar sa kuma yanzu haka rundunar ta dage wurin ganin an yi ma sa adalci.”
“Yayin yaba wa mutanen kirkin jihar Imo, ya tabbatar mu su da cewa rundunar ta na kokarin ganin ta dakatar da rashawa daga duk wani jami’in dan sanda.”

Kwamishinan ya kara da cewa za a sanar da sakamakon binciken ‘yan sandan.

Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000

A wani rahoton, rundunar ‘yan sandan musulunci ta Hisbah a jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa.

A wata tattaunawa da BBC Pidgin ta yi da kwamanda janar na rundunar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya bayyana hakan.

Ibn-Sina ya ce sun kama matashin ne saboda abinda ya aikata ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyauta mai tsoka

Asali: Legit.ng

Online view pixel