Shugaba Buhari ya hadu da Dangote, Abdussamadu, da Tinubu a taron da ya je a Saudi

Shugaba Buhari ya hadu da Dangote, Abdussamadu, da Tinubu a taron da ya je a Saudi

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron jawo hannun jari da ake shiryawa a kasar Saudi Arabia
  • Mai girma shugaban Najeriyar ya zauna da Attajirai irinsu Aliko Dangote da Wale Tinubu a wajen wannan taro

Saudi - A ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hadu da manyan Attajiran kasar nan a kasar Saudi Arabiya.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai da hula da jama’a, Femi Adesina ya fitar da jawabi na musamman yayin da Buhari yake Riyadh.

Femi Adesina yace Mai girma shugaan kasa da tawagar gwamnatin Najeriya sun halarci taron jawo hannun jari da aka shirya a birnin Riyadh, Saudi Arabia.

Adesina ya yi wa jawabin na sa take da ‘President Buhari, Nigerian delegation participate in 5th future investment initiative summit, Riyadh, Saudi Arabia’.

Kara karanta wannan

Labarin Hotuna: Dangote, AbdulSamad, Mangal, Shugaba Buhari sun gudanar da aikin Umrah

Femi Adesina ya fitar da jawabi

Wannan jawabi yana kunshe da labari cewa shugaban kasar ya gana da shugaban kamfanin BUA group, Abdussamad Rabiu da shugaban Oando, Wale Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya hadu da Dangote, Abdussamadu
Shugaba Buhari tare da Dangote da Abdussamadu
Asali: Facebook

Har ila yau, shugaban na Najeriya ya hadu da babban mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu da shugaba/CEO na kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote; da shugaba/wanda ya kafa BUA group, Abdul Samad Rabiu.”

Jawabin ya cigaba:

“Da kuma shugaban kamfanin Oando Plc, Wale Tinubu, a wajen taron jawo hannun jari a Riyadh.” - Femi Adesina.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa daga baya an ga babban ‘dan kasuwan nan na jihar Katsina, Alhaji Dahiru Barau Mangal tare da wadannan Attajirai sun yi Umrah.

Yayin da Dangote ne mutumin da ya fi kowa dukiya a kaf nahiyar Afrika, Abdussamad Rabiu yana tasowa, shi ma mutumin Kanon ya ba fam Dala biliyan 4.5 baya a yau.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

CBN ya shigo da eNaira

Yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin kudin yanar gizo, an ji E-Naira ya shigo da farin-jini sosai, mutane rututu sun sauke manhajar E-Wallets.

Ana sa rai samar da eNaira da bankin CBN ya yi zai bunkasa tattalin arziki ta hanyar karbar haraji da kuma rage kudin da aka kashewa wajen buga takardun kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel