Ka ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda: Shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

Ka ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda: Shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

  • Gwamnoni, yan majalisun tarayya, da yan majalisun jihohin na cigaba da kira ga Shugaba Buhari ya dau mataki kan yan bindiga
  • Abu na farko sun bukaci a daina kiransu da yan bindiga, kawai a rika kiransu da sunan yan ta'adda
  • Sheikh Ahmad Gumi kuwa ya ce kada a kuskura a ayyanasu hakan saboda akwai hadari

Katsina - Shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 sun yi ittifaki wajen kira ga Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya alanta yan bindiga matsayin yan ta'adda.

Wannan ittifaki ya biyo bayan taron gammayar shugabbannin majalisun da ya gudana ranar Lahadi a majalisar dokokin jihar Katsina.

Wannan kira na yan majalisun ya biyo bayan kiran da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, su kayi ga shugaban kasa na ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda.

Read also

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

Shugaban gamayyar Kakakin majalisun wanda shine Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana cewa wannan na cikin abubuwa biyar da suka yarje kai bayan awanni takwas suna tattaunawa.

Yace:

"Muna kira ga shugaba Buhari ya ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda kuma makiya al'umma."
"Gamayyar ta lura da abubuwan da yan bindigan ke yi kuma hakan bai banbanta da na yan ta'adda ba."

Ka ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda: Shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36
Ka ayyana yan bindiga matsayin yan ta'adda: Shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 Hoto: Speakers
Source: Facebook

Source: Legit

Online view pixel