Gwamnatin Buhari ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Sudan

Gwamnatin Buhari ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Sudan

  • Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kasar Sudan da ya faru yau Litinin
  • Ta bukaci a gaggauta daukar matakin dawo da gwamnatin dimokradiyya a kasar nan da nan
  • Hakazalika, manyan hukumomin duniya su ma sun tofa tofin Allah-tsine kan wannan lamari

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Sudan tare da yin kira da a gaggauta sakin firaministan kasar da duk wasu fursunonin siyasa.

Juyin mulkin dai na zuwa ne makonni kadan kafin sojoji su mika shugabancin majalisar da ke mulkin kasar a hannun farar hula.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Esther Sunsuwa, ta kuma yi kira da a gaggauta maido da gwamnatin rikon kwarya tare da aiwatar da taswirar da aka amince da ita don mayar da kasar kan tafarkin dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya

Gwamnatin Buhari ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Sudan
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya ta yi Allah-wadai ga juyin mulkin da ya auku a yau a Sudan, inda sojoji suka rusa bangaren farar hula na gwamnatin rikon kwarya tare da kame shugabanninta.
"Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi kira da a gaggauta sakin firaminista da dukkan fursunonin siyasa tare da maido da gwamnatin rikon kwarya cikin gaggawa da aiwatar da taswirar da aka amince da ita don mayar da kasar ga tsarin dimokuradiyya."

Daily Trust ta ruwaito cewa, wakilin Burtaniya na musamman kan Sudan da Sudan ta Kudu, Robert Fairweather, ya ce kamen da sojoji suka yi wa shugabannin farar hula "cin amanar juyin juya hali ne, da sauyi da kuma al'ummar Sudan".

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da EU da kuma kungiyar kasashen Larabawa sun nuna matukar damuwa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Yanzu haka an rufe filin jirgin saman Khartoum, kuma an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa.

Juyin mulkin na zuwa ne kimanin wata guda bayan hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde na Guniea, kamar yadda AlJazeera ta ruwaito a baya.

Tsauraran matakai 3 da sojoji su ka ɗauka bayan kama Firayim Minista Hamdok

Sakamakon barkewar guguwar juyin mulki a kasar Sudan da ke nahiyar Afirka, manyan sojoji sun jagoranci juyin mulki inda su ka je har fadar Firayim ministan kasar kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Bisa ruwayar Legit.ng, sun isa fadar ta sa da ke Khartoum inda su ka kama PM Abdalla Hamdok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel