Fusatattun Zamfarawa sun mamaye titunan jihar, suna zanga-zangar rashin tsaro

Fusatattun Zamfarawa sun mamaye titunan jihar, suna zanga-zangar rashin tsaro

  • Fusatattun jama'ar jihar Zamfara sun mamaye titunan jihar inda suka hana ababen hawa wucewa
  • Jama'a mazauna karamar hukumar Tsafe sun fito kwan su da kwarkwatarsu wurin tare titin Gusau zuwa Funtua
  • Zamfarawan sun koka da yadda 'yan bindiga suka hana su noma tare da tare su da suke suna kwatar man fetur

Zamfara - Fusatattun mazauna kauyukan karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a ranar Laraba sun rufe babban titin Gusau zuwa Funtua domin bayyana fusatarsu kan al'amuran 'yan bindiga a jihar.

Mazauna yankin sun ce ba za su bar ababen hawa da jama'a wucewa ba har sai an yi maganin kokensu, Daily Trust ta wallafa.

Fusatattun Zamfarawa sun mamaye titunan jihar, suna zanga-zangar rashin tsaro
Fusatattun Zamfarawa sun mamaye titunan jihar, suna zanga-zangar rashin tsaro. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Sun ce duk da datse layukan sadarwa da aka yi a jihar, miyagun 'yan ta'adda sun hana su zuwa gonakinsu, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

Daruruwan ababen hawa ne suka tsaya tare da matafiya suka dinga sauya hanya zuwa inda suke tsammanin za su gujewa masu zanga-zangar.

"Yankuna kamar su Yankuzo, Yan ware, Tafkin Kazai, Hayin Alhaji Yartalata wadanda ke gabashin Tsafe duk suna karkashin ikon 'yan bindiga. Duk da an rage garkuwa da mutane, amma 'yan ta'addan na cigaba da yi wa jama'a fashi.
“Babbar matsalarsu yanzu shi ne yadda za su zuba man fetur a baburansu, A wasu makonni da suka gabata, ina kan babur di na, sai wasu 'yan ta'adda suka tsare ni tare da bukatar man fetur. Dole ta sa na juya domin gujewa fadawa tarkonsu.
“Su kan tsare babura domin karbar man fetur daga jama'a, ba kamar da ba da suke sace mutane tare da bukatar kudin fansa. Da tuni an sace ni a watan da ya gabata," wani mazaunin yankin mai suna Aliyu yace.

Read also

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ba a same shi ba domin tsokaci kafin rubuta wannan rahoto.

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

A wani labari na daban, sama da 'yan bindiga 50 sojojin Najeriya suka ragargaza har lahira sakamakon luguden wuta ta sama da ta kasa a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan nasarar da jami'an tsaron suka samu ta tabbata ne da kokarin dakarun sojin sama da na kasa a yankin Saulawa zuwa Farin Ruwa a karamar hukumar Birnin Gwari.

Kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta samu labari daga rundunar hadin guiwar, jirgin yaki na sojojin sama ne suka samar da taimako ga dakarun sojin kasa da ke kusantar yankin Dogon Dawa zuwa Damari zuwa Saulawa.

Source: Legit.ng

Online view pixel