Gwamna El-Rufai zai fara hana ma'aikatan da basu yi rigakafin Korona ba shiga ofis

Gwamna El-Rufai zai fara hana ma'aikatan da basu yi rigakafin Korona ba shiga ofis

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana matakin da za ta dauka kan dukkan wadanda basu yi rigakafin Korona ba
  • Gwamna ya ce dole ne ma'aikatan gwamnati kowa ya yi rigakafi kafin ranar 31 ga wannan watan
  • Hakazalika, masu ziyartar ofisoshin gwamnati ma za a bukaci su yi rigakafin ko su nuna shaidar sun yi

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarin daukar mataki kan ma'aikatan gwamnatin jihar da ba su yi allurar rigakafin Korona ba.

Wata sanarwa da gwamna El-Rufai ya fitar a shafinsa na Facebook dauke da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ta bayyana dalilin daukar matakin.

Da Duminsa: El-Rufai zai fara hana ma'aikatan da basu yi rigakafin Korona ba shiga ofis
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai | Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Gwamnatin ta ce, daga ranar 31 ga watan Oktoba za a hana ma'aikatan gwamnatin da basu yi allurar rigakafi ba shiga ofisoshin gwamnati.

Kara karanta wannan

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin domin tabbatar da ba da kariya ga yaduwar kwayar cutar Korona a cikin al'umma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"Tun tuni Ma'aikatar Lafiya ta fara yin allurar rigakafi ga dukkan ma'aikatan gwamnati, kuma ana sa ran kammala wannan kafin ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2021. Ana bukatar dukkan ma'aikatan gwamnati su yi allurar rigakafin kafin wannan ranar."

Hakazalika, gwamnatin ta ce, dukkan baki da za su ziyarci ofisoshin gwamnati za su bukaci gabatar da shaidar yin allurar rigakafin na Korona.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Masu ziyartar ofisoshin gwamnati za su bukaci gabatar da katunan shaidar rigakafin su.
"Ganin karancin wadatattun alluran rigakafin da ake samu a halin yanzu, baki da ba su riga sun yi allurar rigakafin ba, a cikin dan lokaci, za a ba su izinin shigowa tare da gabatar da shaidar rajista tare da Ma'aikatar Lafiya ta jihar da nufin yin allurar rigakafin, yayin za su ci gaba da sanya takunkumin fuska."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta soke hukumomin man fetur uku, kuma ta sallami shugabanninsu, ga jerinsu

Insha Allahu bana yan Najeriya zasu yi aikin Hajji, Hukumar jin dadin Alhazai NAHCON

A wani labarin, Hukumar jin dadin alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa da yardar Ubangiji bana maniyyata a Najeriya zasu samu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji.

Wannan ya biyo bayan soke dokokin kariya daga cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Saudiyya tayi a farkon makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel