Gwamna El-Rufai ya bayyana abun da yayi wanda har ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu

Gwamna El-Rufai ya bayyana abun da yayi wanda har ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana yadda ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu saboda shirin yi wa malaman jihar gwaji
  • Gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya so sadaukar da komai nasa don ganin yara sun samu ingantaccen ilimi a jiharsa
  • El-Rufai ya bayyana cewa ya fuskanci barazana game da shan kaye a zabe amma ya ce lallai sai an yi wa malaman gwaji don kawai ya cimma manufarsa

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi bayanin yadda ya so sadaukar da kudirinsa na zarcewa a karo na biyu don bai wa yaran jiharsa ilimi mai inganci.

Da yake magana a wani taro da aka gudanar a Ado-Ekiti, jihar Ekiti, El-Rufai ya ce an yi masa barazana da shan kaye a zabe, Channels TV ta ruwaito.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Gwamna El-Rufai ya bayyana abun da yayi wanda har ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu
Gwamna El-Rufai ya bayyana abun da yayi wanda har ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu
Source: Facebook

El-Rufai ya ce ya dage sannan ya aiwatar da gwajin kan malamai a Kaduna duk da barazanar.

“An ce dan uwana a nan ya fadi takararsa na biyu a karon farko saboda yayi barazanar yiwa malamai gwaji.
“Na gwada su sannan na sallame su kafin zabenmu. Da aka ce mun zan rasa kujerana a karo na biyu, nace idan rasa kujeran zai ba yaran jihar Kaduna makoma mai kyau da ilimin firamare mai inganci, toh na shirya hakura da shi.”

El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA

A wani labari na daban, Malam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya nada Khalil Nur Khalil mai shekaru 28 a matsayin shugaban cibiyar habaka zuba jari ta jihar Kaduna, KADIPA.

Khalil ya kammala digirinsa daga jami'ar Eastern Mediterranean da ke kasar Cyprus inda ya karanci kasuwanci da tattalin arziki.

Read also

Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi

TheCable ta ruwaito cewa, kafin wannan nadin, Khalil ne daraktan zuba jari a KADIPA, matashi mafi karancin shekaru da ya taba samun wannan matsayin a tarihin jihar Kaduna.

Source: Legit.ng

Online view pixel