El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA

El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nada matashi mai shekaru 28 matsayin shugaban cibiyar habaka zuba jari ta Kaduna
  • Khalil Nur Khalil kyakyawan matashi ne da ya kammala digirinsa a fannin kasuwanci da tattalin arziki a jami'ar Cyprus
  • Khalil ya rike daraktan cibiyar, matsayin da zama matashi mafi karancin shekaru da aka taba rikewa a tarihin jihar Kaduna

Kaduna - Malam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya nada Khalil Nur Khalil mai shekaru 28 a matsayin shugaban cibiyar habaka zuba jari ta jihar Kaduna, KADIPA.

Khalil ya kammala digirinsa daga jami'ar Eastern Mediterranean da ke kasar Cyprus inda ya karanci kasuwanci da tattalin arziki.

TheCable ta ruwaito cewa, kafin wannan nadin, Khalil ne daraktan zuba jari a KADIPA, matashi mafi karancin shekaru da ya taba samun wannan matsayin a tarihin jihar Kaduna.

Read also

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA
El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

A sanarwar da aka fitar a ranar Litinin, Muiywa Adekeye, mai bada shawara na musamman ga El-Rufai a fannin yada labarai ya sanar da sauye-sauyen da aka samu a bangaren mukamai a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adekeye ya ce, Muhammad Sani Abdullahi, shugaban ma'aikata, an mayar da shi ma'aikatar tsari da kasafi.

Jaafaru Sani, Thomas Gyang, Halima Lawal, Ibrahim Hussaini, Shehu Usman Muhammad, Muhammad Sani Abdullahi, Kabir Mato da Idris Nyam an mayar da su ma'aikatun muhalli, ayyuka, ilimi, noma, kananan hukumomi, kasuwanci, kirkire-kirkire da wasanni daya bayan daya.

An nada Balaraba Aliyu Inuwa a matsayin mai gudanarwa ta birnin Zaria, Muhammad Hafiz Bayero a matsayin mai gudanarwa na birnin Kaduna da Phoebe Sukai Yayi a matsayin mai gudanarwa ta Kafanchan.

An nada Umma Aboki a matsayin babbar sakatariyar ma'aikatar tsari da kasafi, Murtala Dabo a matsayin shugaban hukumar kasafin kudi da kuma Abubakar Hassan a matsayin darakta janar na hukumar lafiya ta jihar Kaduna.

Read also

Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa

An nada Tamar Nandul a matsayin manajan darakta na hukumar habaka kasuwanni da kamfanoni a jihar Kaduna, Maimunatu Abubakar a matsayin babbar manajan cibiyar kiyaye muhalli ta jihar Kaduna.

Ba a samu sauyi a ma'aikatun kudi, shari'a, lafiya, gidaje da habaka birane, tsaron cikin gida da sauransu, TheCable ta ruwaito.

Terere: Yadda Bishop Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

A wani labari na daban, Shugaban cocin Living Faith Worldwide wanda aka fi sani da Winners Chapel International, Bishop David Oyedepo, an bayyana shi daga cikin 'yan Najeriya da suka kafa kamfanoni a tsibirin Turai na Virgin.

Premium Times ta ruwaito cewa, sunan Oyedepo ya bayyana a cikin takardun Pandora wanda kungiyar 'yan jarida ta International Consortium of Investigative Journalists (ICIJ) suka jagoranta.

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi, Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Osun duk sun bayyana a cikin 'yan siyasan da suka washe kudin kasa suka adana a Turai.

Read also

Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP

Source: Legit

Online view pixel