Aliko Dangote: Jerin Jami’o’i 7 da Suka Karrama Attajirin Najeriya da Digirin Girmamawa

Aliko Dangote: Jerin Jami’o’i 7 da Suka Karrama Attajirin Najeriya da Digirin Girmamawa

  • Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya samu karramawa daga manyan jami’o’i saboda gudunmawarsa a kasuwanci da jin kai
  • Tun daga Najeriya har zuwa Birtaniya, wadannan jami'o'i sun gamsu da tasirin Dangote kan cigaban tattalin arziki da zamantakewa
  • Mun tattaro jami'o'in da suka ba Dangote digirin girmamawa, suna murnar nasarorin da ya samu da kuma tasirinsa ga al'umma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Attajiri na biyu da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya samu karbuwa a duniya saboda irin gudunmawar da ya ke bayarwa ga masana’antu da kuma ayyukan jin kai.

Tasirinsa ya wuce a kwatanta, kamar yadda manyan jami'o'i masu daraja suka ba shi digirin girmamawa da yawa duk don saboda bajintarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ɗauki mataki na gaba bayan ganawa a Abuja

Jami'o'i 7 sun karrama attajirin Najeriya, Aliko Dangote da digirin girmamawa
Aliko Dangote ya samu digirin girmamawa akalla 7 daga jami'o'i. Hoto: Pius Utomi Ekpie
Asali: Getty Images

Jami'o'in da suka ba Dangote digirin Dakta

Legit Hausa ta duba jami'o'i bakwai da suka karrama Dangote da digirin girmamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Jami'ar Ibadan, Najeriya

A shekarar 2016, jami’ar Ibadan, daya daga cikin manyan jami'o'in Najeriya ta ba Aliko Dangote digirin girmamawa a fannin kimiyya, inji rahoton The Sun.

Wannan karramawa ta shaida ce ga gagarumar gudunmawar da ya bayar ga tattalin arzikin Najeriya da kuma taimakon jama’a, musamman a fannin ilimi da kiwon lafiya.

2. Jami'ar Coventry, Birtaniya

Jami'ar Coventry da ke Birtaniya ta karrama Dangote da digirin girmamawa a fannin kasuwanci duk a shekarar 2016 kamar yadda jami'ar ta sanar a shafinta na intanet.

Karramawar ta bayyana irin gagarumar gudunmawar da ya ke bayarwa ga harkokin kasuwanci a duniya da kuma rawar da ya ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki a Afirka.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Muhimman dalilai 5 da suka sa ASUU ta yi barazanar rufe jami'o'i a Najeriya

3. Jami'ar ABU, Zariya, Najeriya

Mun ruwaito cewa jami’ar Ahmadu Bello, daya daga cikin manya kuma tsofaffin jami'o'i a Najeriya, ta ba Dangote digirin girmamawa a shekarar 2019.

Wannan karramawar ta nuna irin yadda ya ke gudanar da harkokin kasuwanci da kuma sadaukar da kai wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyoyi daban-daban.

4. Jami’ar Bayero, Kano, Najeriya

Tun a shekarar 2016, jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya ta ba Dangote digirin girmamawa.

Wannan karramawa ta kasance mai nuna bajintar gudunmawar da ya bayar a fannin masana'antu da kuma ayyukansa na jin kai.

5. Jami'ar Dundee, Birtaniya

Jami'ar Dundee da ke Birtaniya ta karrama Dangote da digirin girmamawa a shekarar 2019.

Jami'ar ta karrama shi ne saboda tasirinsa a kasuwanci da sadaukar da kai ga ci gaban al'umma.

6. Jami’ar jihar Nasarawa, Najeriya

Jami’ar Jihar Nasarawa ta ba Aliko Dangote lambar yabo ta digirin girmamawa bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa tattalin arziki da walwalar jama’a.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Wannan karramawar ta bayyana kokarinsa na samar da guraben ayyukan yi da tallafawa ayyukan ilimi musamman a jihar.

7. Jami'ar Nnamdi Azikiwe, Najeriya

Jami’ar Nnamdi Azikiwe ta ba Dangote lambar yabo ta digirin girmamawa bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da ayyukan alheri.

Ta yaba da rawar da Dangote ke takawa wajen bunkasar tattalin arziki da kuma jajircewarsa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya da dama.

Taimakon da Aliko Dangote yake yi a jami'o'i

A wani labarin, mun ruwaito cewa attajiri Aliko Dangote ya fitar da Naira biliyan 1.5 domin gina dakin kwanan dalibai a jami'ar Ahmadu Bello.

Tun a shekarar 2019 aka yi kiyasin cewa Dangote ne mutum daya tilo da ya fi zuba jari a bangaren jami'o'in Najeriya, wanda ke samun yabo kan kokarinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.