Jami’ar Ahmad Bello za ta ba Aliko Dangote shaidar Digirin Dakta

Jami’ar Ahmad Bello za ta ba Aliko Dangote shaidar Digirin Dakta

Mun ji cewa babbar jami’ar nan ta Ahmadu Bello wanda aka fi sani da ABU da ke cikin Garin Zariya, za ta karrama wasu manyan da su kayi fice a wajen bikin yaye ‘Dalibanta da za tayi wannan karo.

Jami’ar za ta ba Alhaji Aliko Dangote shaidar Digirin Dakta a wajen wannan babban biki da za ayi. Rajistran wannan fitacciyar jami’a ta Najeriya, Malam Ahmed Abdullahi Kundila, shi ne ya fito ya bayyanawa Duniya wannan.

A jawabin AA Kundila a madadin hukumar makarantar, ya bayyana cewa Jami’ar ta ABU ta zabi ta ba Aliko Dangote wannan kyauta ne ganin irin kokarin da yake yi na taimakawa mutane da kuma habaka tattalin arzikin Najeriya.

Za ayi wannan taro ne a Ranar Asabar 27 ga Watan Afrilu inda jami’ar za ta yaye ‘daliban ta 15, 289 da su ka kammala karatun Digiri da kuma Difloma. Daga cikin ‘Daliban akwai fiye da 4, 486 wadanda su kayi Difloma, da Digirgir da Digir-digir.

KU KARANTA: Buhari ya samawa mutane fiye da Miliyan 12 aikin yi - Lai

Jami’ar Ahmad Bello za ta ba Aliko Dangote shaidar Digirin Dakta

Aliko Dangote zai samu kyautar Dakta daga Jami’ar Ahmadu Bello
Source: Depositphotos

Har wa yau, an samu ‘dalibai 81 cikin sama da 10, 000 da su ka kammala Digirin farko, da su ka gama da ajin farko da matakin Digiri watau “First Class.” Za a kuma ba zakakuran Daliban da su kayi fice a kowace tsangaya babbar kyauta.

Ana sa rai cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, da kuma Ministan ilmi na kasa, Malam Adamu Adamu, za su halarci wannan taro da za ayi.

Jami’ar za kuma ta karrama tsohon shugaban hukumar kwadago na kasa na NLC, Kwamared Hassan Adebayo Sunmonu da shaidar Dakta tare da Aliko Dangote wanda ya ginawa jami’ar dakuna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel