Jerin manyan jami'o'i guda biyar mafi girma a Najeriya
Shin ka taba tunanin, jami'ar da tafi kowacce girma a Najeriya? Wannan rahoton zai bayyana maka duka abinda ya kamata ka sani game da jami'o'in da suka fi girma a Najeriya
Duk da dai girma jami'a ba wai shine abinda zai saka dalibi ya zabe ta ba a matsayin inda zai yi karatu, amma dai wannan labari yana da matukar amfani.
Idan har kana son sanin jami'ar da tafi girma karanta ka gani jerin jami'o'i guda biyar a Najeriya da muka samo:
1. Jami'ar Ilorin - Kadada 15,000
Wacce ta zama ta daya a cikin jerin jami'o'in ita ce jami'ar Ilorin. Ita ce jami'ar da tafi kowacce girma a Najeriya, inda take da girman kadada 15,000.
KU KARANTA: Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara
2. Jami'ar Abuja - Kadada 11,824
Jami'ar Abuja tana nan akan babbar hanyar Kaduna - Abuja - Lokoja, ita ce ta zama ta biyu a cikin jerin jami'o'in, inda take da girman kadada 11,824.
3. Jami'ar Noma ta Tarayya dake Abeokuta - Kadada 10,000
An samar da jami'ar a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1988, girman jami'ar ta noma ta gwamnatin tarayya dake Abeokuta ya kai kadada 10,000.
4. Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria - Kadada 7,000
An samar da jami'ar ABU a ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 1962, a farko sunan jami'ar shine Jami'ar Arewacin Najeriya. Tana da girman kadada 7,000.
5. Jami'ar Obafemi Awolowo - Kadada 5,260
Jami'ar na da girman kadada 5,260. Yawan daliban na ta karuwa a kowacce shekara daga 244 a shekarar 1962 zuwa sama da mutum 30,000 a yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng