Dangote yafi kowane dan Najeriya zuba jari a jami’o’in Najeriya, inji gwamnatin tarayya

Dangote yafi kowane dan Najeriya zuba jari a jami’o’in Najeriya, inji gwamnatin tarayya

-Aliko Dangote ya kafa tarihi a bangaren jami'o'in Najeriya, inda ya zuba jarin N1.2b domin gina dakin kwanan dalibai a wata jami'a dake Najeriya

-Tsawon shekaru 70 da kafa jami'a a Najeriya ba'a taba samun mutum daya da yayi irin wannan aikin da Dangote yayi ba

Gwamnatin tarayya a jiya ta bayyana cewa dakin kwanan dalibai wanda kudinsa ya kama N1.2b da Aliko Dangote ya gina a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria babu gudumawa tamkarsa da mutum guda ya taba baiwa Jami’ar Najeriya.

Shugaban hukumar jami’o’i ta kasa wato NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed wanda shi ya wakilici shugaba Buhari yayin kaddamar da wannan katafaren dakin kwanan dalibai mai suna Aliko Dangote Hall ya bayyana farin cikin gwamnatin tarayya bisa ga wannan cigaba.

Dangote yafi kowane dan Najeriya zuba jari a jami’o’in Najeriya, inji gwamnatin tarayya
Dangote yafi kowane dan Najeriya zuba jari a jami’o’in Najeriya, inji gwamnatin tarayya
Asali: UGC

KARANTA:Hukumar kula da gidajen yari ta kori babban Ofisa saboda safarar kwayoyi

Shugaban kasan yace: “ Ka yi abinda babu wani dan Najeriya da ya taba yi tun shekarar 1948 da aka bude jami’a ta farko a kasar nan. Wannan shine gudumawa mafi girma daga wajen mutum guda a fadin kasar nan tsawon shekara 70 kenan da kasancewar jami’a a Najeriya. A don haka ina taya Alhaji Aliko Dangote murna.”

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna wanda ya kasance tsohon dalibin jami’ar ne, ya jinjinawa Alhaji Aliko Dangote bisa kafa wannan gagarumin tarihi a jami’ar tasu.

Ya kara da cewa, gudumuwar da Dangote ke badawa musamman cikin lamuran ilimi basu misaltuwa, tabbas ya cancanci a yaba masa.

Ana shi jawabin, shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Ibrahim Garba cewa yayi jami’ar tasu ba zata mance da sunan Dangote ba saboda wannan kyauta da yayi masu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel