Labari ma zafi: Ganduje ya sauya wa KUST Wudil suna zuwa jami'ar Aliko Dangote

Labari ma zafi: Ganduje ya sauya wa KUST Wudil suna zuwa jami'ar Aliko Dangote

  • Gwamna Ganduje ya sauya wa jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kano da ke Wudil suna zuwa jami'ar Aliko Dangote
  • Hakan ya biyo bayan shawarin da kwamitin ziyarar jami'a ya mika wa gwamnatn jihar ta Kano karkashin Gwamna Ganduje
  • Gwamnan ya amince da hakan ne a zaman majalisar zartarwa na jihar na karshe da aka yi inda yace jami'ar ta koma ADUST, Wudil

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta amince da sauya suna jami'ar jihar Kano ta kimiyya da fasaha, KUST, da ke Wudil zuwa jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote.

Solacebase ta ruwaito cewa, majalaisar zartarwar jihar ta amince da hakan ne a zaman karshen da ta yi wanda Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya jagoranta.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda yace wannan cigaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin ziyarar jami'ar ta bayar.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Ganduje ya sauya wa KUST Wudil suna zuwa jami'ar Aliko Dangote
Ganduje ya sauya wa KUST Wudil suna zuwa jami'ar Aliko Dangote. Hoto daga solacebase.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takarda ta ce daga yanzu sunan jami'ar, jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote, ADUST, da ke Wudil, Kano.

Takardar ta kara da bayanin cewa, an mika takardar amincewar da gwamnan yayi ga majalisar jihar domin su duba dokokn kafa jami'ar sannan su gyara.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel