Ku kalla da kyau na gaske ne ba ciko ba - Rahama Sadau ta karyata zargin da ake mata na sanya mazaunan roba

Ku kalla da kyau na gaske ne ba ciko ba - Rahama Sadau ta karyata zargin da ake mata na sanya mazaunan roba

- Fitacciyar jaruma Rahama Sadau ta karyata mujallar da ta kalubalance ta akan cewa tana amfani da bayan roba

- Wannan lamari dai ya biyo bayan wasu hotuna da jarumar ta sanya a shafinta na sada zumunta wadanda suka jawo hankalin mutane da yawan gaske

- Mujallar dai ta bayyana cewa jarumar ta yi amfani da bayan roba, inda ita kuma ta fito ta bayyana cewa na gaske ne babu ciko

Fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta karyata mujallar fim da ta kalubalance ta akan cewa tayi amfani da bayan roba a lokacin da ta dauki wani hoto mai daukar hankali a babban birnin tarayya Abuja.

Shafin na mujallar fim din ya sanya hoton Rahama Sadau din da ta dauka, inda suka rubuta cikin harshen turanci 'Real or Fake, Flesh or Plastic', ma'ana anya kuwa na gaskiya ne wannan baya nata.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Mujallar fim ta kalubalanci Rahama Sadau da amfani da mazaunan roba a wani hoto da ta dauka

Ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai ga jarumar Rahama Sadau ta mayar musu da martani da cewa "Na gaskiya ne, sai kuma Hamdala."

Wannan hoto da jaruma Rahama Sadau ta dauka ta sanya a shafinta na sada zumunta sun jawo hankalin mutane da dama. Jarumar dai ta dauki wannan hoto ne a lokacin bikin kyakkyawa kuma mafi karancin shekaru a 'yan siyasar kasar nan Munira Tanimu, wacce aka sha shagali a birnin Abuja watannin da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel