Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya

Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya

'Yan siyasa suna ta kai da komowa domin ganin sun janyo ra'ayin masu jefa kuri'a musamman yanzu da babban zaben 2019 ya matso kusa. Wasu 'yan siyasan na ta sauya sheka zuwa jam'iyyun da suke ganin za su basu tikitin takara.

Hakan yasa 'yan siyasar ke amfani da daburu daban-daban wajen ganin cewa sunyi nasarar lashe zabukan da ke zuwa.

A yau, Legit.ng ta kawo muku biyar daga cikin dabarun da 'yan siyasa ke amfani dasu wajen janyo ra'ayin masu kada kuri'a domin yin nasara a zaben.

1) Cudanya da talakawa

'Yan siyasa daga sassan Najeriya da dama suna amfani da wannan dabarar musamman idan zabe ya karato.

Abinda su keyi shine za su rika shiga cikin talakawa suna cudanya da su tare da aikata wasu abubuwan da basu saba yi a baya ba kawai domin talakawar su amince da su kuma suyi tsamanin 'yan takarar za su cigaba da kusantarsu bayan zabe.

Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya
Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya
Asali: Twitter

Za ka ga hotunan 'yan siyasan na shiga kasuwani suna sayaya ko kuma cin abinci irin wanda talakawa ne suka saba cin wadannan abincin.

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

2) Siyasar cika ciki

Siyasar ciki wanda ke nufin rabawa masu kada kuri'a kayan abinci ya shahara ne a 2014 lokacin zaben gwamna a jihar Ekiti, inda gwamna Ayodele Fayose mai barin gado ya rabawa masu zabe shinkafa kuma ya yi nasara a zaben.

Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya
Dabaru 5 da 'yan siyasa ke amfani da su domin lashe zabe a Najeriya
Asali: UGC

Daga baya sauran 'yan siyasa daga jam'iyyu da yawa sun kwaikwayi wannan tsari inda suke rabon kayayakin abinci domin nasarar zabe.

3) Karyar Talauci

Wasu daga cikin 'yan siyasa sun gano cewa hankalim talakawa ya fi kwanciya da dan takarar da ya taso cikin talauci da gwagwarmaya domin suna ganin shine zai fi tausayin talakawa.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi amfani da wannan dabarar inda ya yi ikirarin cewa ya taso cikin talauci da yunnwa har ta kai ga bashi da takalmin lokacin da ya ke zuwa makaranta.

4) Sayar kuri'u

Wannan tana da kamanceceniya da Siyasar cika ciki sai dai a nan kudi zalla ake amfani da shi wajen sayan kuri'an masu zabe. Wannan shima ba sabon abu bane amma lamarin ya zama ruwan dare a cikin wannan shekarar musamman a zaben gwamna na jihar Ekiti a 2018.

5) Yarjejeniya da iyayen siyasa

Ita kuma wannan cuwa-cuwar tana faruwa ne lokacin da wani jigo a jam'iyyar ya yi yarjejeniya da wani dan takara domin ya taimaka masa ya lashe zabe.

Dama iyayen gidan siyasa su ne masu fada a aji a jam'iyya, za su iya amfani da kudi, mulki da wasu dabaru domin su kafa duk dan takarar da suke so daga baya shi kuma dan takarar zai yi musu sakayya bayan ya dare kan mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel