Kano: Ana Rade-radin Tube Shi a Sarauta, Ado Bayero Zai Kaddamar da Gagarumin Aiki Don Talaka

Kano: Ana Rade-radin Tube Shi a Sarauta, Ado Bayero Zai Kaddamar da Gagarumin Aiki Don Talaka

  • Ana cikin cece-kuce kan matsayin kujerar Sarkin Kano, Ado Bayero zai kaddamar da wani gagarumin aiki a jihar
  • Sarkin zai kaddamar da asibitin kungiyar Musulunci ta Ahmadiyya Muslim Jama’at a birnin Kano
  • Kaddamar da sabon asibitin zai gudana ne a gobe Asabar 20 ga watan Janairu wanda zai iya daukar marasa lafiya 100 a rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero zai kaddamar da sabon asibitin Ahmadiyya Muslim Jama’at a birnin Kano.

Kaddamar da sabon asibitin zai gudana ne a gobe Asabar 20 ga watan Janairu wanda zai iya daukar marasa lafiya 100 a rana, cewar Tribune.

Sarkin Kano zai kaddamar da gagarumin aiki don talaka a jihar
Ado Bayero zai kaddamar bude sabon asibiti a Kano. Hoto: Aminu Ado Bayero.
Asali: Facebook

Mene Sarkin Kano, Ado Bayero zai kaddamar a Kano?

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari kauyen Zariya, sun sace uwa da ɗanta, mijin ya tsere

Asibitin da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri har ila yau, Sarkin ne ya kaddamar da kafa tubalin gina asibitin a watan Yulin shekarar 2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda kungiyar Musuluncin ta ce a cikin wata sanarwa, Sarkin zai samu rakiyar sarakuna da ke yankinsa, World Top News ta tattaro.

Sauran wadanda ake sa ran za su halarci taron sun hada da masu mukamai a gwamnatin jihar da Tarayya da FRSC da kuma hukumar NDLEA.

Kiraye-kirayen da ake yi a Kano kan tube Sarkin Kano

Kungiyar Musulunci ta Ahmadiyya Muslim Jama’at ta gina asibitinta na farko a shekarar 1950 a Apapa da ke Legas da kuma Kano a shekarar 1962.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta cece-kuce kan ruguza masarautun Kano da tsohon gwamnan jihar, Abdulllahi Ganduje ya kirkiro.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

Kiraye-kirayen mayar da tsohon Sarki, Sunusi Lamido sun fara tasiri wanda idan hakan ta tabbata zai maye gurbin Sarki Aminu Ado Bayero.

Da alamu Sunusi Lamido zai koma kujerarsa

A wani labarin, ana ta kiraye-kirayen mayar da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi kan kujerarsa.

Kiraye-kirayen sun fara tasiri a jihar tun bayan cin zaben Gwamna Abba Kabir a matsayin gwamnan jihar a watan Maris.

Wannan ya biyo bayan tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir a matsayin halastaccen gwamnan jihar a Kotun Koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.