Gwamnan APC Ya Yi Magana Yayin da Fitaccen Malamin Musulunci Ya Rasu a Arewacin Najeriya

Gwamnan APC Ya Yi Magana Yayin da Fitaccen Malamin Musulunci Ya Rasu a Arewacin Najeriya

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya yi alhinin rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a jihar Gombe, Khalifa Sheikh Muhammadu Kobuwa ranar Jumu'a
  • Fitaccen malamin addinin musuluncin ya rasu ne da safiyar ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024 kuma tuni aka masa jana'iza
  • Gwamna Yahaya ya ce wannan babban rashi ne ba ga al'ummar jihar Gombe kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran ɗarikar Tijjaniya a jihar, Khalifa Sheikh Muhammadu Kobuwa.

Kamar yadda jaridar Tribune Online ta tattaro, Gwamna Yahaya ya nuna matuƙar alhini da wannan babban rashi da aka yi na Shehun Malami, wanda ya rasu ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addinin Musulunci ya riga mu gidan gaskiya a Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Gwamnan APC Ya Yi Magana Yayin da Fitaccen Malamin Musulunci Ya Rasu a Arewa Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana marigayin a matsayin babban malamin addinin musulunci kuma ginshikin Tijjaniya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen aikin ibada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar gwamnan, marigayi Khalifa Kobuwa mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen bautar Allah da yaɗa akidu da dabi’un Annabi Muhammad (SAW).

Inuwa Yahaya ya ce:

"Tasirin Sheikh Muhammadu Kobuwa ba zai gushe ba a zukatan al’umma musamman mabiya darikar Tijjaniyya. Haka kuma yadda yake jagorantar al'amura da koyarwarsa abun koyi ne ga mutane da dama."

Gwamnan ya ci gaba da cewa, "Rasuwarsa babban rashi ne ba ga jihar Gombe kadai ba, har ma da kasa baki daya.

"Ina fatan waɗanda ya tafi ya bari zasu ɗora daga inda ya tsaya a kan kyawawan ayyukansa na alheri da hikima, domin ci gaba da koyar da jikokin mu masu zuwa nan gaba."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a jihar Arewa, an yi wa mataimakin gwamna ihu

Gwamna Yahaya ya yi ta'aziyya ga Musulmai

Daga nan sai gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ‘yan uwa ƴan Fiyanul Islam, kungiyar Tijjaniyya, da sauran al’ummar musulmi baki daya.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya jikansa da Rahama, ya saka masa da gidan Aljannar Firdausi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan harkokin yaɗa labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar ranar Jumu'a.

Wane gwamna ƴan bindiga suke hari?

A wani rahoton kuma Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin abin harin yan bindiga saboda ya hana su rawan gaban hantsi a Katsina.

Dikko Radda ya faɗi haka ne jim kaɗan gabanin shiga taron tsaro na sirri da ya kira cikin gaggawa kan tsadar rayuwa da kuma ƙalubalen tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel