Sarkin Musulmi Ya Tafka Rashi Har 2 a Rana 1 Kwanaki Kadan Bayan Bikin Sallah

Sarkin Musulmi Ya Tafka Rashi Har 2 a Rana 1 Kwanaki Kadan Bayan Bikin Sallah

  • Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar ya tafka babban rashi yayin ya rasa 'ya'yan 'yan uwansa guda biyu
  • Allah ya karbi rayuwar Hussaini S. Adiya da kuma Mu'azu Sulaiman wadanda suka rasu a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu
  • Wannan babban rashi na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan gudanar da bukukuwan karamar sallah a jihohin Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - An shiga jimami bayan Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya rasa ’ya’yan yan uwansa biyu a rana ɗaya a garin Sokoto.

Wannan rashi na zuwa kwanaki uku da gudanar da bukukuwan salla karama a fadin Najeriya baki ɗaya.

Sarkin Musulmi ya yi rashin 'yan uwa guda 2 a rana guda
Sarkin Musulmi ya yi babban rashi bayan rasuwar 'yan uwansa guda 2 a rana guda. Hoto: Muhammad Sa'ad Abubakar.
Asali: Twitter

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya rasa yara

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da fitaccen dan jarida a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Daily Trust ta tattaro cewa Sarkin Musulmi ya yi rashin manyan 'yan uwansa guda biyu a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda suka rasu akwai Hussain S. Adiya da kuma Mu’azu Suleiman wadanda suka rasu a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu.

Mu’azu ƙani ne ga tsohon ministan wasanni, Yusuf Suleiman wanda ya rasu jim kadan bayan sallar asuba, cewar rahoton 21st Century Chronicles.

Sai kuma Hussaini wanda tsohon babban sakatare ne a wata ma'aikata a gwamnatin jihar Sokoto ya rasu bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.

Gudanar da jana'izar 'yanuwan Sarkin Musulmi

Tuni aka yi musu sallar jana'iza a masallacin Sultan Bello da ke Sokoto inda Sarkin Musulmi da manyan mutane suka halarta.

Har ila yau, an binne su a makabartar gidan sarautar Sokoto na Hubbaren Shehu kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Jami'ar rundunar sojojin Najeriya ta yi babban rashi a birnin Abuja

Basarake ya rasu bayan ɗarewa karagar mulki

A baya, kun ji cewa wani basarake ya rasa rayuwarsa watanni 11 bayan ɗarewa kujerar sarauta a jihar Ondo.

Marigayin mai suna Julius Omomo da ke sarautar Oda ya rasu ne a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu ya na da shekaru 83 a duniya.

Daya daga cikin 'yan uwan marigayin shi ne ya tabbatar da mutuwar basaraken a jiya Lahadi 14 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel