Mutum 5 sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon hatsarin mota a hanyar Ondo

Mutum 5 sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon hatsarin mota a hanyar Ondo

- Mummuna hadarin mota ta faru a hanyar Owo zuwa Akure a jihar Ondo tsakanin wasu motocci biyu

- Hadarin motar ta yi sanadiyyar rasuwar mutane biyar yayin da mutum takwas sun samu rauni

- Kwamandan hukumar FRSC na jihar ya tabbatar da afkuwar hadarin inda ya ce gudu fiye da ka'ida da rashin kyawun birki ne ya janyo hatsarin

Mutane biyar sun riga mu gidan gaskiya sannan wasu mutane takwas sun samu raunuka sakamakon hadari mota da ya faru a jihar Ondo a ranar Talata.

Hadarin ya faru ne a lokacin da wata babban mota mai lamba AKD 88o XX ta fada wa wata mota J5 mai lamba LSR 855 XF a Emure a kan hanyar Owo-Akure a jihar ta Ondo.

Mutum 5 sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon hatsarin mota a hanyar Ondo
Mutum 5 sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon hatsarin mota a hanyar Ondo. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, na jihar Ondo, Ahmed Hassan ya tabbatar da afkuwar hatsarin a ranar Talata a Akure, babban birnin jihar.

Hassan ya ce yawan gudu da rashin kyawun birki a bangaren mai babban motar ne ya yi sanadin hadarin.

DUBA WANNAN: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Ya ce, "Motocci biyu ne hadarin ya ritsa da su a Karamar hukumar Ewure na jihar.

"Mutum 13 ke cikin motoccin biyu, guda biyar sun mutu nan take yayin da takwas kuma sun jikkata.

"An kai wadanda suka yi raunin zuwa Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Owo, yayin aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dajin ajiye gawa."

A kalla hadarin mota biyar sun faru a jihar cikin watanni biyu da suka shude inda aka rasa rayyuka.

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin manyan mambobin kungiyar ƴan daba ta marigayi Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana wanda ya ce sunansa 'Manjo' ya ce za su cigaba da gwagwarmaya duk da shugabansu ya mutu.

Ya ce marigayi Gana ya ji a jikinsa cewa zai mutu hakan yasa ya mika shugabancin ga wanda ke biye masa a ƙungiyar sa kafin zuwa rungumar shirin afuwa filin motsa jiki na Atongo a Katsina-Ala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel