Ga mulki ga Sarauta: Sarkin Gombe zai naɗa gwamnan jam'iyyar APC Sarauta
- Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa gwamnan jihar, Inuwa Yahaya sarautar gargajiya
- Sarkin ya tura tawagar mutum 8, bisa jagorancin tsohon gwamnan Bauchi, Ahmed Muazu, domin isar da sako ga gwamnan
- Gwamna Yahaya, ya bayyana jin daɗinsa bisa wannan girmamawa daga mai martaba sarkin Gombe ya masa
Gombe - Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu III, zai naɗa gwamna Inuwa Yahaya na jihar, sarautar 'Ɗan maje,' kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Hukumar dillancin Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa sarkin ya aike da tawagar mutum takwas, karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Muazu, tsohon gwamnan Bauchi, domin sanar da gwamnan, ranar Lahadi.
Muazu ya bayyana cewa sarkin ya ɗauki wannan matakin ne domin girmama gwamnan bisa namijin ƙoƙarin da yake yi a Gombe, Aminiya ta rahoto.
Meyasa sarki ya naɗa gwamna Yahaya Sarauta?
Da yake mika takardar naɗin gwamna Yahaya, shugaban tawagar, Ahmed Muazu, yace:
"Sarki ya gamsu da kokarin gwamna a ɓangaren ilimi, kiyon lafiya, gina hanyoyin da kuma tsaftace gari."
"Hakanan kuma munga yadda gwamnati ta yi kokari wajen rage rushewar gidaje saboda ambaliyar ruwa."
"Mun zo nan ne domin gabatar da wannan sarauta da sarki ya naɗa ka, kuma ziyarar mu ba ta da alaƙa da siyasa."
Gwamna Yahaya ya nuna jin daɗinsa
A nasa jawabin, gwamna Yahaya yace:
"Ina mika godiya ga Allah mai girma da ɗaukaka bisa wannan sarauta da ya bani daga mai martaba Sarkin Gombe."
"Wannan sarauta da aka bani zata ƙara mun azamar ƙara dagewa da yiwa mutanen jihar Gombe aikin da ya dace."
"Wannan babbar girmamawa ce da Allah ya bani, kuma ba zan baiwa sarki da sauran al'ummar jihar Gombe kunya ba."
A wani labarin kuma Jam'iyyar Hamayya PDP ta lallasa APC mai mulki a zaɓen karamar hukumar Kajuru
Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta lallasa jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen ƙaramar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.
Baturen zaɓen yankin, Dakta Ibrahim Dan Maraya, ya bayyana ɗan takarar PDP, Honorabul Ibrahim Gajere, a matsayin wanda ya lashe zaɓe.
Asali: Legit.ng