Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili

Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Abia sun kama wani tsoho mai shekaru 70, Marcel Udeh, kan zargin aikata kisan kai
  • Ana zargin Udeh ya kashe 'dan cikinsa a yankin karamar hukumar Umunneochi saboda ya cinye abincin da ya rage masa a tukunya
  • Kakakin 'yan sandan jihar Abia, Maureen Chinaka,ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce za a gurfanar da shi da zaran an kammala bincike

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Abia - Rahotanni sun kawo cewa wani mutumi mai suna Marcel Udeh, ya kashe 'dansa saboda abinci, a karamar hukumar Umunneochi ta jihar Abia.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Udeh, mai shekaru 70 wanda ya fito daga kauyen Eziama Lokpaukwu, ya gano cewa 'dansa ya cinye abincin karshe da ya rage masa a tukunya.

Kara karanta wannan

"Ban san me ya hau kaina ba": Matashi ya sheke mahaifiyarsa, ya kona gidansu

Uba ya kashe dansa a Abia
Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Cike da fusata, Udeh ya shiga cikin dakinsa sannan ya fito da bindiga ya harbe 'dan nasa, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa, da faruwar lamarin sai mutanen garin suka kama Mista Marcel sannan suka daure masa hannayensa tare da daura shi kan gawar 'dan nasa.

Rundunar 'yan sanda ta yi martani

Da take martani kan lamarin, Maureen Chinaka, kakakin 'yan sandan jihar Abia, ta ce an kai rahoton lamarin sashin 'yan sandan Umunneochi, inda ta kara da cewar an kama wanda ake zargin.

Chinaka ta ce:

"Eh, mun samu wani rahoto a sashin Umunneochi.
"An kama wanda ake zargin kuma yanzu haka an mika lamarin zuwa sashin binciken laifuka na jihar don gudanar da bincike.
"Za a gurfanar da shi a kotu bayan nan."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Matashi ya kashe mahaifinsa a Filato

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani matashi dan shekara 29 mai suna, Joseph Yakubu, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa, Yakubu Dalyop.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ƴan sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa taɓarya, kuma daga karshe rai ya yi halinsa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Filato, Hassan Steve Yabanet, ne ya sanar da hakan a hedkwatar ƴan sanda ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel