Mark Zuckerberg Ya Zarce Bill Gates a Arziki, Dangote Ya Samu Ribar Dala Biliyan 1 a Mako 1

Mark Zuckerberg Ya Zarce Bill Gates a Arziki, Dangote Ya Samu Ribar Dala Biliyan 1 a Mako 1

  • Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, yanzu shine mutum na hudu mafi arziki a duniya bayan ya samun ribar dala biliyan 36
  • Zuckerberg ya shiga gaban wanda ya kafa kamfanin Microsoft, wato Bill Gates kuma yanzu yana kusa da Bernard Arnault.
  • Wannan na zuwa yayin da attajirin Najeriya Aliko Dangote ya samu ribar dala biliyan 1 mako guda bayan asarar dala biliyan 5

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg yanzu ya zama mutum na hudu a jerin attajirai a duniya, inda ya zarce wanda ya kafa Microsoft, wato Bill Gates.

Alkaluman da hukumar Bloomberg ta fitar sun nuna cewa, da farko Zuckerberg ya yi asarar dala biliyan 5 da ya yi a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

Mark Zuckerberg ya koma na hudu a jerin masu kudin duniya.
Mark Zuckerberg ya koma na hudu a jerin masu kudin duniya. Hoto: JOSH EDELSON / Contributor
Asali: Getty Images

Amma yanzu Zuckerberg ya sha gaban 'yan uwansa Amurkawa, inda yake da dala biliyan 165 idan aka kwatanta da dala biliyan 145 na Bill Gates.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuckerberg ya tashi daga matsayin na 20 a mafi arziki a duniya

Zuckerberg ya tashi daga matsayi na 20 a mafi arziki a duniya a cikin zango na biyu na 2023 don zama na hudu bayan samun ribar kusan dala biliyan 37.

Kwanan nan ne majalisar dokokin Amurka ta tuhumi Zuckerberg kan laifuffukan da kamfanonin sa na sada zumunta suka yi.

Attajirin ya kasance a matsayi na hudu a duniya bayan Bernard Arnault, tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya.

A farkon watan Janairu wanda ya kafa Amazon Jeff Bezos ya hambarar da Arnault a matsayin na biyu mafi arziki a duniya yana bin bayan shugaban kamfanin Tesla Elon Musk.

Kara karanta wannan

Talaka zai ji a jikinsa sakamakon tashin kudin shigo da kaya da aka yi wa Kwastam

Akwai tserayar dala biliyan 15 tsakanin Zuckerberg da Elon Musk, wanda ya yi asarar kusan dala biliyan 30 yayin da farashin hannun jarin Tesla ya sauka.

Dangote ya samu ribar dala biliyan daya cikin kwana bakwai

Masu sharhi sun yi imanin cewa arzikin Zuckerberg ya canza bayan da hannun jari na Meta ya tashi tun a farkon shekara, inda ake cinikayyar duk hannu jari daya akan $459.41.

A hannu daya, attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya, Aliko Dangote ya samu ribar kimanin dala miliyan 59 a cikin sa’o’i 24 da suka wuce da kuma dala biliyan 1 a cikin kwanaki bakwai.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Dangote ya yi asarar dala biliyan 5.4 bayan da aka ce Najeriya ta karya darajar kudinta a karo na biyu cikin watanni takwas.

Dangote ya yi asarar dala biliyan 5 a cikin sa'o'i 24

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta ruwaito attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya da Afrika, Aliko Dangote, ya sauka daga na 81 zuwa na 113 cikin sa'o'i 24 a jerin masu kudin duniya.

Wannan ya biyo bayan asarar dala biliyan 5.4 (Naira tiriliyan 7) da attajirin ya yi a ranar Alhamis 1 ga Fabrairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel