Yadda Muke Koyawa Marasa Jin Magana Karatu da Haddar Kur’ani Inji Malamin Kurame

Yadda Muke Koyawa Marasa Jin Magana Karatu da Haddar Kur’ani Inji Malamin Kurame

Kaduna - A halin yanzu, wasu Bayin Allah suna kokarin ganin kurame sun koyi karatun Al-Kur’ani mai tsarki a Zariyan jihar Kaduna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Malami
Malamin da yake koyar da kurame Hoto: Yasir Sulaiman Kofa
Asali: Facebook

Yasir Sulaiman Kofa suna da makarantar kurame a gidan Malam Dahiru Kanti a Unguwar Iya a birnin Zazzau da ‘yan yara suke yin hadda.

A unguwar Tudun wada, akwai wata makarantar addinin musulunci da ake koyar da Kur'ani da darusa ga manyan dalibai; matasa zuwa tsofaffi.

Legit ta samu zantawa da Ustaz Yasir Sulaiman Kofa wanda ya yi mana bayanin yadda suke bi wajen kai Al-Kur’ani ga marasa jin magana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za ka iya fada mana takaitaccen tarihinka?

Kara karanta wannan

Shari’o’in takarar gwamnoni 3 mafi zafi da za a kawo karshensu yau a Kotun Koli

Sunana Yasir Sulaiman Kofa, an haife ni a unguwar Zabarmawa da ke kofar Doka, a birnin Zariya. Na yi karatun boko da addini a garin Zariya; nayi firamare a Kwarbai a lokacin, daga nan na tafi sakandare a Al-Hudada a Zariya. Bayan nan na tafi Nuhu Bamalli Polytechnic nayi karatun sharar fage na IJMB zuwa jami’a. Da na kammala, ban samu gurbin shiga jami’a ba, sai a ‘yan wadannan shekarun ne yanzu na ke karatun ilmin kimiyyar komfuta a jami’ar ABU Zariya.

A bangaren addini, na yi karatu a karkashin malamai da yawa, na yi karatu a makarantar Ihya’ As-Sunnah, da makarantar Minhaj Al-Islam a Kwarbai.

Ina aka samu karatun kurame?

Abin akwai ban al’ajabi, wata rana na fito zan je koyon komfuta, sai na hadu da wani malamina wanda yace zai yi mani tallar wani karatu da za ayi, idan ina so, in zo in halarta, sai na fasa zuwa komfutar, muka tafi aka gabatar da karatun kurame. Na koyi yaren kurame ne a makarantar Islamiyya amma da Ingilishi.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

Mecece mu’amalar malam da kurame kafin nan?

Gaskiya wata alaka ba ta taba hada ni da kurame ba. Asali ma ko a cikin danginmu babu kurame gaba daya.

Wani hali kurame suke ciki?

Gaskiya rayuwar kurma akwai ban tausayi. A lokacin da muka taso idan ka ga kurma sai dai a wajen markade, wankin mota da sauran ayyukan wahala da barace-barace.

Meyasa ku kayi tunanin koyawa kurame Kur’ani?

Dalilin da ya sa muka yi wannan tunani shi ne muna samun korafi da yawa. A duk lokacin da muka fita yin wa’azin kurame, sai ya kasance mafi yawan tambayoyin da ake yi mana shi ne yadda za a karanta Kur’ani mai girma.

Ta ya aka koyi yaren kurame?

Mun tuntubi kuramen domin jin yadda za a koyi karanta Kur’ani yadda aka sauke shi, sai suka fada mana sai dai a samu wani a tura shi zuwa kasar Sudan, Misra ko Saudiyya, sai a koyi karantun domin a koyar da su. A lokacin mun rubuta takardu zuwa fada, gidan gwamnati da wuraren malamai domin a dauki nauyin malamai su koyi karatun. Wannan ne dalilin da ya sa muka fara koyon karatun ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfana a kotu kan zargin taba muhibbar malamin addini a Kano

Kur’ani kadai ake koya masu?

A’a, kafin mu fara koyar da su Kur’ani, sai da muka soma da littattafan addini dabam-dabam. Alal misali akwai lokacin da muka fassara littattafan fikihu da na sirah da sauransu zuwa Ingilishin kurame. Ta kai ta yadda kurma zai iya daukar littafi ya fahimci addini.

Wani hali ake ciki?

Daga baya ne muka gane akwai Kur’ani da larabcinsu, dole karanta littafi mai tsarki sai da larabci, hakan ya sa muka kauda turancin nan. Yanzu kokarin da ake yi kenan, idan Allah SWT ya yarda, nan gaba da zarar kurma ya ga bakin larabci, zai fahimta har ya karanta.

Dalibai nawa ku ke da su?

Gaskiya, dalibanmu suna da yawa, akwai wadanda muka killace a gida. Akwai wadanda suke waje, irinsu sai karshen shekara muke haduwa ayi taro na musamman a kan addini kamar sanin Allah SWT, tsarki da sauransu. Mu kan gayyato shahararren malami ya yi masu karatu, mu kuma sai mu fassara masu. Ba za mu iya cewa ga yawan daliban ba. Karatunmu ya kunshi manya, yara, matasa, mata da tsofaffi.

Kara karanta wannan

N585m: EFCC ta titsiye Akanta Janar kan zargin badakalar Sadiya Farouk da Betta Edu

Wasu kalubale ake fuskanta?

Tun da ba a karbar kudin makaranta ko na rajista kuma babu wata kungiya da ke daukar nauyinta, makaranta ce ta sa-kai da aka hadu aka kafa domin ilmantar da wadannan mutane. Idan malami ya ga babu wani albashi illa dawainiya, zai iya tafiya. A dalilin haka malamai suka ragu daga bakwai zuwa hudu.

Nasarorin da aka samu

A sanadiyyar wannan kokari kuramen da ake koyawa Kur’ani sun halarci gasar duniya da aka shirya ta kafar Google Meet a kasar Saudi, kuma masu gudanar da musabakar sun yi na'am da salon da muka dauka, suka ba su shaidar halarta. Mu ne karon farko na kasar bakar fata da ta halarci wannan taron. Kuma sai da muka yi wa dalibai akalla 35 rajista.

Menene yake sa ka farin ciki?

Idan na tuna da wannan karamin kokarin da muka yi, sai farin ciki ya lullube ni. Mu kanmu Allah SWT ne ya zabe mu da baiwarsa domin akwai tafintocin kurame fiye da 500 masu rajista. Abin farin ciki ne mutum ya koyi Kur’ani ta hannunka. A cikin dalibanmu akwai masu shekaru 40 ko 50 da ba su iya Suratul Fatiha, duk wanda yake wurin ya zubar masu da hawaye.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun koma fada da juna, an tarwatsa yaran mashahurin ‘dan ta’adda

Kana da wani buri?

Daga cikin burina shi ne kurma ya iya koyon larabci sannan kuma in ga kurma ya haddace Kur’ani, ina rokon Allah SWT ya cika mani wannan buri kafin in cika.

Wani kira malam yake da shi?

Nauyi ne a kan gwamnati da ‘yan siyasa su dauki dawainiyar ilmantar da kurame addini, kuma hakan ba zai yi mata wahala ba. Ba mu fata nan da 2030, ya zama akwai wani kurma da bai iya karatun Al-Kur’ani ba.

Kur'anin Kurame a Najeriya

Kwanakin baya aka ji yadda kungiyar Al-Furkan da wata takwararta a Najeriya suka hada-kai aka kaddamar da Kur’ani domin kurame.

Ustaz Yasir Sulaiman Kofa ne ya jagoranci wannan aiki wanda aka shafe har kwanaki bakwai ana yi a garin Zariya a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel